BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Masu tarzoma na wawashe kaya da ƙone dukiya a Faransa

Tarzoman ta fara ne a kan kisan da wani dan sanda ya yi wa wani matashi dan shekara 17

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Bayan da aka yi kwana na uku a jere ana ta tarzoma a Faransa, a kan kisan da wani dan sanda ya yi wa wani matashi dan shekara 17 da ke tuka mota, rahotanni na nuna cewa masu tarzomar na wawashe dukiya da kona kaya sassan kasar musamman Paris.

Ana iya ganin irin mummunar illar da masu tarzomar suka yi wa tituna, inda suka kona motoci da wawashe kantuna a birnin, duk da dokar hana fita da aka sanya.

Hukumomi sun ce an kama mutane sama da 667 an kuma da raunata ‘yan sanda da jama'a.

Bayan kwana uku da soma wannan zanga-zangar wadda ta fara cikin lumana da ruwan sanyi domin neman a yi adalci ga kisan matashin, Nahel, ranar Talata da safe, zanga-zangar ta rikide ta zama tarzoma, inda ta yadu a sassan kasar ta Faransa har ma zuwa makwabciya Belgium.

Dubban jama’a ne ciki har da mahaifiyar matashin da dan-sandan ya harbe a wata unguwar bayan gari da ke babban birnin, Paris, Nanterre suka shiga zanga-zangar a birnin da sauran sassan kasar.

Lauyan iyalan matashin Yassine Bouzrou, ya gaya wa BBC yadda hankalin iyalan ya tashi a kan kisan dan nasu:

Ya ce: ''Hankalin iyayen Nahel ya tashi sosai. Suna cikin kaduwa, kuma abu ne mawuyaci gaya a gare su jure ma wannan abu.''

Masu tarzomar sun rika dauki-ba-dadi da ‘yan sanda lamarin da ya kai ga raunata jama’a da ma jami’an tsaron.

Zuwa safiyar Alhamis rahotanni da kafafen yada labaran kasar ke bayarwa na nuna cewa an dan samu lafawar tarzomar a sassan babban birnin kasar ta Faransa, Paris.

Can ma a Belgium mai makwabtaka inda zanga-zangar ta bazu wasu rahotanni na cewa an kama mutum 15 a babban birnin kasar, Brussels.

Dan sandan da ya harbi matashin, ya rasu wanda tuni aka kama shi tare da tuhumarsa da laifin aikata kisa, ya nemi gafara daga iyayen da ‘yan uwan matashin kamar yadda lauyansa Laurent-Franck Liénard ya fada.

Lauyan ya ce shi kansa, dan sandan hankalinsa ya dugunzuma a kan hoton bidiyon da ya ga ni na tashin hankalin, yana mai cewa ba wai yana tashi ba ne haka kawai da safe ya shiga kashe mutane.

Ya ce kalmarsa ta farko da ya furta ita ce, a yi hakuri haka kuma kalmarsa ta karshe ita ce hakuri ga iyalan.

Hukumomi dai sun baza ‘yan sanda dubu 40 a fadin kasar ta Faransa, yayin da jiragen kasa da motocin bas na sufurin birane suka dakata da aiki da wurwuri a yankuna da dama.

‘Yar majalisar dokokin kasar da ke wakiltar yankin da dan sandan ya harbe matashin Prisca Thevenot, wadda ‘yar jam’iyyar Shugaba macron ce ta musanta zargin cewa akwai wariyar launin fata a aikin dan sanda a kasar, kamar yadda wasu ke danganta kisan da aka yi wa matashin da nasabar wariyar launi.

Source: BBC