Red Bull ta nada mataimakin kociyan Liverpool, Pepijn Lijnders a matakin wanda zai yi kociyan kungiyar.
Mai shekara 41, wanda ya karbi aikin Anfield a 2014, zai horar da kungiyar dake buga gasar Australia kan yarjejeniyar kaka uku.
Lijnders, wanda yake aiki karo na biyu a kungiyar Anfield, zai bar kungiyar dake buga Premier League, sakamakon da Jurgen Klopp zai ajiye aikin bayan 19 ga watan Mayu.
Kociyan ɗan kasar Netherlands na son horar da salon kai hare-hare a kungiyar dake buga babbar gasar tamaula ta Australia.
Tun farko Lijnders, wanda ya yi aiki karkashin Brendan Rodgers, ya taka rawar gani a Liverpool har da a karkashin Kloop, wanda aka dauka aiki a cikin Oktoban 2015.
Ya ajiye aikin kungiyar Anfield ya koma horar da NEC Nijmegen ta Netherlands, amma wata bakwai tsakani ya sake komawa Liverpool.
Mai kula da bunkasa wasannin Liverpool, Vitor Matos zai je Australia tare da Lijnders a matakin mataimakin koci.