Kamfanin Darul Mus'haf na ɗaya daga cikin kamfanonin buga Al Ƙur'ani mafi girma a nahiyar Afrika.
Kamfanin na daya daga cikin gine-gine mafiya girma a birnin Khartoum na ƙasar Sudan.
A shekarar 1994 ne aka bude gidauniyar kafa kamfanin Darul Mus'haf kuma ta samu tallafi daga bangarori da dama a ciki da wajen Sudan.
Kamfanin ya samu kafuwa a shekarar 2001 da burin samun lada ta hanyar samar da Al Ƙur'ani ga miliyoyin Musulmi 'yan Afrika da ke fama da talauci ƙarƙashin International Univerity of Africa ko Jam'atul Ifriƙiyyal Alamiyya.
Kamfanin Darul Mus'haf na buga Al Ƙur'ani aƙalla 100,000 duk wata.
Bugun rubutun Al Ƙur'ani mataki-mataki ne, daga shirya rubutun a komfuta zuwa wurin ɗinkewa.
Shirya rubutu da zayyanar shafuka
Wannan shi ne mataki na farko, inda ake shirya yadda rubutun zai fito a shafukan Al kur'anin da irin kwalliyar da za a yi a jikinsa a kan komfuta.
AbdelRaazeq Yusef, babban jami'i a kamfanin ya bayyana cewa akwai salon rubutu da zayyana iri iri da su ke amfani.
"Wasu daga cikin waɗannan salon mun samo su ne daga Saudiyya, wasu daga Syria wasu ma daga Indunesiya," a cewarsa.
"Don haka mu kan zaɓa wanda mu ke so da kuma irin launin da za mu yi kwalliyar da shi, ko ja ko ruwan ƙwai ko kalar makuba," in ji shi.
Sai dai ya ce wannan iyakar kwalliyar ko zayyanar shafukan ne kawai.
"Rubutun Al ƙur'ani dole da baƙar tawwada ake yin sa, haka tsarin ya ke. Don shi mutane su ka fi jin daɗin karantawa," in ji AbdelRaazeq Yusuf.
Haka kuma, a wannan matakin ne ake aikin bitar rubutun da zai fito a shafukan Al Ƙur'ani.
AbdelRaazeq ya ce akwai malami a ƙalla guda 10 zuwa 11 da ke aikin duba rubutun. Amma ba a lokacin guda su ke yi ba.
"A matakin farko mu na ba malamai biyar ɗaya bayan ɗaya su duba rubutun. Idan wannan ya duba sai ya ba wannan," in ji shi.
Ya ce idan wadannan malaman zubin farko sun duba kuma sun yi na'am da shi ko kuma sun yi gyare gyare a kai, sa a ba wasu jerin malamai shidda kuma su ma su sake dubawa.
Kuma ko wanne daga cikin waɗannan malaman za su sa hannu cewar sun duba iyakar iyawarsu.
Ana yin haka ne duk don a guje wa samuwar wani kuskure a rubutun ayoyin na littafin mai tsarki.
Bayan wannan matakin ne kuma sai a je mataki na gaba, wato matakin gurza rubutun daga na'urar gurzawa.
Matakin gurza rubutun Al Ƙur'ani
A wannan matakin, akwai wata na'ura da ke aiki da kemikal da ƙaro da ruwa inda ake sa wata takarda mai kauri wacce ke ɗauke da zayyanar da ake so.
A wannan matakin ne kuma ake zaɓar launin da zayyanar za ta fito.
Haka kuma, baya ga takardar mai kaur akwai wani shafi na ƙarfen aluminium mai ɗauke da kwalliyar da ɗigon ayoyi da ke fitowa a kan shafukan Al Ƙur'ani.
Don haka ana ɗora shafin ƙarfen ne a kan takardar mai kauri don ta naɗi rubutun da ke jiki. Ita kuma da ita ake amfani wurin fitar da zayyanar a kan ainihin shafin AlƘur'ani.
Shirya takardu a na'ura da kuma bugawa
A nan, akwai na'urori biyar a jejjere kuma a haɗe da juna. Ko wacce ta dogara da ɗayar.
A na'urar farko a na shirya takardun da rubutun Al Ƙur'anin zai fito a kai. Takardun manya ne masu kimanin faɗin sentimita 50 a kan ko wacce ana samun shafin madaidaicin Al Ƙur'ani 16.
Na'urar ce ta ke shirya takardun sannan tana fitar da su ɗaya bayan ɗaya tana aikawa da su na'ura ta gaba.
Ita kuma tana ɗauke da wani sinadari da ke goge takardan kuma yana sa ta ƙyalli.
Daga nan ne sai takardar ta gangara na'ura ta gaba wadda ke ɗauke da tawaddar da ke yi rubutu a kan shafukan. A wannan matakin ne rubutu da kwalliyar jikin shafin ke fitowa.
Sai na'ura ta gaba mai dauke da gam wadda ke harhada takardun wuri guda. Sannan na'ura ta ƙarshe mai fitar da takardun bi da bi, wato shafi biye shafi.
Yanka takardu da kuma ɗinke su
Da zarar an fitar da takardun daga na'urar da ke jera su, akwai wata babbar na'ura wadda ke ɗauke da manyan ƙarafuna masu kaifin gaske.
Ana kiran ɗakin da wannan na'ura take da suna tiyata.
Wadannan ƙarafunan ne ke yanka shafukan nan 16 zuwa dai dai girman da ya dace sannan ta shirya su shafi bayan shafi.
Daga nan kuma akwai na'ura ta daban wadda aikinta shi ne dinkewa ko liƙe takardunsu zama kundi guda.
A wannan matakin, akwai abubuwan da da hannu ake yinsu, kamar like bangon Alƙur'anin. Akwai ma'aikata na musamman da aikinsu kenan, wato amfani da gam wajen harhaɗa shafukan AlƘur'anin.
A lokacin bugawa, wani lokaci a kan samu shafukan da ke fitowa ba daidai ba ko kuma a samu kuskure a bugun shafukan.
Akwai ma'aikatan da aikinsu shi ne duba irin waɗannan kuma Idan aka samu irin haka, a kan ware waɗannan shafukan a tara su a wani ƙaton bokiti sannan daga baya a ƙona su.
A kamfanin Darul Mus'haf, Akwai nau'ikan girman Al Ƙur'ani biyu wato da babba da ƙarami.
Kuma a Darul Mus'haf a na aiki ne da ruwayoyi biyar amma yanzu waɗanda mu ke bugawa su ne ruwayar Duri da Hafs da Warshu.
Babban jami'in kamfanin, AbdelRaazeq Yusef ya ce suna alfahari da kamfanin na Darul Mus'haf ko ba komai, ya ce miliyoyin Musulmi a faɗin Afrika na karanta Al Ƙur'anin da suka buga.
Kuma ya ce a baya bayan nan ma, sabuwar shugabar Tanzania, Samai Suluhu Hassan ta sha rantsuwar shugabancin ƙasarta da ɗaya daga cikin Al Ƙur'anin da aka buga a wannan kamfani.