Menu

Matan Sri Lanka masu aikatau a Saudiyya na neman agaji saboda uƙubar da suke ciki

 118269028 Gettyimages 187734395 Akwai 'yan ci-rani daga kasar Sri Lanka kusan 500,000 a Saudiyya kuma galibinsu mata ne

Sun, 2 May 2021 Source: BBC

Shekarun Thushari 16 lokacin da mahaifiyarta ta bar ta a gida Sri Lanka zuwa kasar Saudi Arabia a matsayin 'yar aikin gida.

Hakan ya faru ne a cikin watan Maris na shekarar 2019.

Tun daga wancan lokacin ba ta sake ganin mahaifiyarta Sunethra, mai shekaru 43 ba.

Akwai 'yan ci-rani daga kasar Sri Lanka kusan 500,000 a Saudiyya kuma galibinsu mata ne da aka dauka a matsayin masu aikin gida.

Amma kuma, watanni takwas bayan isar ta kasar Saudiyya, ta bar aikin nata a matsayin mai aikin gida.

Yanzu tana nan a makale a cibiyar da ake tsare bakin haure, tare da sauran mata 'yan kasar Sri Lanka 40, da kungiyar Amnesty International ba ta jima da wallafa labarin halin da suke ciki ba.

Thushari ta shaida wa BBC ta wayar tarho cewa "Mahaifiyata ta fuskanci mayuwcin hali a hannun wadanda suka dauke ta aiki. Ba ma a biyan ta. Ba isasshen abinci."

"Wata rana an taba kulle ta a cikin ban daki har na tsawon wuni guda, ba tare da shan ruwa ba."

Sunethra ta yanke shawarar barin gidan, kuma a bisa dokar kasar Saudiyya, nan da nan ta zama bakuwar haure.

Masu aikin gida daga kasashen waje na bukatar daukar nauyi daga wadanda suka dauke su aiki kafin a amince su zauna a kasar ta Saudiyya.

Jim kadan bayan tserewarta, 'yan sanda suka cafke ta suka kulle ta a cibiyar da ake tsare bakin haure, kuma tun daga wancan lokacin tana ta jiran lokacin da za a a tasa keyarsu gida Sri Lanka.

Kananan yara da mata masu juna biyu

Thushari ta tsorata da abubuwan da ta ji game da cibiyar tsarewar kuma tana tunanin irin halin da mahaifiyarta ke ciki.

"Mata 40 ne a cikin daki daya, amma babu isasshen fili na ko da mutane goma a can. A wasu lokutan sukan yi fada a kan samun gurbin zama.

"Cikin su akwai kananan yara da mata masu juna biyu da kuma tsofaffi.''

Kamar yadda kungiyar Amnesty International ta bayyana, an tsare matan Sri Lankan 41 din tare da wasu kananan yara masu watanni takwas zuwa 19 a cibiyar da ake tsarewar a Riyadh babban birnin kasar ta Saudiyya.

"Mata uku na da kananan yara a tare da su, kuma akwai daya matar da ke bukatar agajin kiwon lafiya na gaggawa. Babu ko da guda a cikin su da aka bayyana musu irin laifukan da suka aikata, kana babu wani taimako ta fannin shari'a da za su iya gane dalilan da suka sa a ka tsare su," kungiyar ta bayyana a wata sanarwa.

Rashin samar da bayanai

Kose Mohiddeen Anzar, wani dan kasar Sri Lanka dan ci-rani a kasar ta Saudi Arabia ya ce shi ne ya tunkari kungiyar ta Amnesty International, bayan da kokarin da ya yi na rokon mahukunta ya gaza cimma nasara.

"Akwai 'yan kasashe da dama a cibiyar, amma mahukunta daga sauran kasashen na daukar matakai, don haka ana tasa keyar wadancan matan. 'Yan Sri Lanka ne kadai ake bata lokaci," ya shaida wa BBC.

Mr Anzar ya sha ziyartar cibiyar, amma ba yarda ya gana da wadanda ake tsare da su din ba.

"Ba su san duk wani abin da ke faruwa a waje ba," in ji shi.

"Ba a son ran gwamnatin Saudiyya ba ne take tsare da su a nan. Saboda rashin kulawar gwamnatin Sri Lanka ne ya sa har yanzu suke a nan."

Dokar korona

Mijin daya daga cikin matan da ake tsare da su ya shaida wa BBC cewa mahukunta a Sri Lanka sun sha bayyana cewa dokar korona ce dalilin da ya sa aka samu tsako wajen mayar da su gida.

Jeyaprakash, dan asalin yankin Tamil a kasar Indian, ya ce ya tunkari ofisoshin yanki har ma da ofsihin shugaban kasa yana neman taimako don a mayar da matarsa gida.

"Matata ba ta samun isassshen abinci ko ruwan sha. Ba ta iya zama sosai saboda tana fama da ciwon basir," a cewarsa.

Yayin da babu wani yunkuri na gaggawa daga mahukuntan Saudiyya, Ministan Kwadago na kasar Sri Lanka Nimal Siripala De Silva ya shaida wa manema labari cewa sun gudanar da tattaunawa da mahukuntan Saudia kuma za a dauki matakin mayar da su gida ba da dadewa ba.

Amma kuma, ba a bayyana takamaimen lokacin ba.

'Ma'aikata da suka fi fuskantar barazana'

Lokacin da Sunethra ta tafi kasar Saudi Arabia a matsayin mai aikin gida, ta bar mahaifiyarta da daukar dawainiyar 'yayanta mata uku.

Mijinta, wanda ke fama da cutar koda, ba shi da tsayayyen aiki kuma ba zai iya yin aikin karfi ba.

Amma a yayin da ake tsare da Sunethra a wannan cibiya har na tsawon fiye da shekara daya, mahaifiyarta ta rasu a ranar 11 ga watan Fabrairu.

Iyalan yanzu na fatan akalla ta samu lokacin da za a yi taron addu'a watanni uku tun bayan mutuwar ta, wani muhimmin taro a bisa al'adar mabiya addinin Buddha.

Kungiyar Amnesty International ta ce Sunethra da sauran matan da ake tsare da su sun yi nuni da matsayin masu aikin gida kan shiga da cewa su ne daya daga cikin mafi fuskantar barazana da hadari a kasashen yankin Gulf da suka hada da kasar Saudi Arabia.

"Garanbawul na baya bayan nan kan aikin kwadago a kasar ta Saudi Arabia, ya cire masu aikin gida, da hakan ke nufin ba za su iya barin kasar b aba tare da izinin wadanda suka dauke su aiki ba, wanda ya haifar musu da karin barazana da cin zarafi da taka hakkin su,'' in ji kungiyar a wata sanarwa.

Tun bayan mutuwar kakarta, Thushari babbar 'yar, ta fara daukar nauyi a matsayin 'mahaifiya' da kuma mai kula da kannenta mata.

Ta ce a saboda haka ba za ta iya neman aiki ba.

"Bayan na dawo daga makaranta, na kan je wajen koyon darasin aikin soja. Ina so in zama sojan ruwa," ta shaida wa BBC, "amma yanzu ba zan iya barin gida ba."

An boye sunayen matan da iyalansu a wannan labarin saboda kare mutuncin su.

Source: BBC