Menu

Matar da ba ta jin zafi ko an yanki fatar jikinta

15117862 Hoton alama

Sat, 3 Jun 2023 Source: BBC

Kwararru sun ce sun gano yadda rikidewar kwayoyin halitta da ba kasafai ake gani ba ya bai wa wata mata damar yin rayuwarta ba tare da jin zafi ba ko an yanki fatar jikinta.

Masu bincike sun kwashe shekara 10 kafin gano yadda kwayoyin halitta ke sauyawa. A shekara ta 2013, wani aiki da aka yi a hannun matar mai shekaru 65 da haihuwa, Jo Cameron, ya sa an gano cewa kwayoyin hallitar ta sun rikide inda hakan ke hana ta jin zafin rauni.

Ta shaida wa BBC cewa, "An yi min tiyatar maganin amosanin gabbai a hannuna, da nake hira da mai aikin jinya, sai ya ce wannan aikin mai zafi ne sosai kuma bayan an gama za ka ci gaba da kasancewa cikin ciwo mai tsanani."

"Sai na ce, ba za ayi haka ba, ba na jin zafin rauni," bayan an gama tiyatar ya zo ya same ni ya tambaya, "ko kin sha wani magani ne. wannan abin mamaki ne."

A lokacin da likitan Dr Devjit Srivastava ya ga cewa da gaske ba ta jin komai, sai ya aika ta zuwa wurin likitoci a jami'ar Landan da kuma Jamia'r Oxford.

Tawagar likitocin suka dauki jininta domin su gudanar da bincike kan kwayoyin halittar da ke jikinta.

Bayan sun kwashe shekaru shida suna bincike sai suka gano cewa sauyawar kwayoyin hallita mai suna FAAH-OUT da ke jikin Ms Cameron, shi ke hana ta jin zafin rauni da tsoro.

Mene ne rikidewar kwayar hallitar FAAH-OUT?

Kwayar hallita mai suna FAAH-OUT tana tattare a cikin kwayoyin hallitun da aka dade ana tunanin cewa ba su da amfani.

Amma yanzu masana kimiyya sun fara sanin muhimmancin wadannan kwayoyin halittar a bangarorin rayuwa kamar su haihuwa da tsufa da kuma cuta.

A wannan yanayin, masu bincike sun iya gano ko wane nau'in kwayoyin halitta ke da alaƙa da rashin jin zafin rauni, da kwayoyin halittan da ke taimakawa wajen guje wa jin tsoro da damuwa, kuma wasu nau'in kwayoyin halitta ne ke taimaka wa Jo ta warke da sauri.

Sun gano cewa sauyawan kwayan halittan FAAH-OUT na rage masa karfi, wanda shi ne ya jibanci jin zafi, da tunani. sauyawan ya na kuma rage yawan yadda ake sarrafa sinadarin FAAH.

Kwayar halitar FAAH da ke jikin Jo na da wani sauyi wanda ke ragewa sinadarin karfi. Yana aiki wurin sarrafa sinadarin protein. Ya kan sarrafa wani sinadari mai suna anandamide wanda ba ya aiki yadda ya kamata a jikin ta.

Masana sun sake ganowa cewa sauyin kwayar halitta biyu da Jo ke da su ba rashin jin zafi kadai su ka shafa ba, amma suna da dangantaka da warkewa.

"Akwai yadda su ke hade da sauran kwayoyin jikin ta, ta na iya warkewa da sauri, kusan kashi 20 zuwa 30 fiye da yadda aka sani, ba karamin abin mamaki ba ko da idan ka dube shi daga bangaren warkar da rauni ne kadai " in ji Dr Andrei Okorokov, mataimakin farfesa a jami'ar UCL kuma babban marubucin binciken da aka wallafa a mujallar 'Neurology Brain'.

"Sauyin na goge wani bangare na kwayar halittar FAAH-OUT ya kuma rufe shi.

Har ila yau Jo na da wani sauyin kwayar halittar FAAH. Ya zuwa yanzu, ba mu san wani a duniya da ke dauke da duka biyun ba."

Me ya sa muke buƙatar jin zafi?

Ciwo yana da mahimmanci don kare mu daga abubuwan da za su iya sa mu fuskanci barazana a rayuwa. Sakamakon rashin jin zafi na iya zama mai matukar muni.

Jo, wadda sau dayawa ta kan kona hannunta yayin da take girki, sai dai ta dogara da jin kaurin konewan fatar ta kafin ta san cewa jikin ta na konewa.

"Mun yi aiki tare da wasu marasa lafiya wadanda su ma ba sa jin zafi ta dalilin sauyin wasu kwayoyin halitta, kuma wani lokaci sukan ji raunuka masu tsanani.

Don haka, jin zafi abu ne mai kyau amma wani lokaci ciwo zai iya zama mai matukar tsanani sai ya zame mara amfani." in ji James Cox, farfesa a jami'ar UCL kuma marubucin binciken.

Lokacin da take tasowa, Jo ba ta da masaniya cewa akwai wani abu daban game da ita. Ba ta taba shan wani abu don taimaka mata ta shawo kan ciwo ba.

"Ban yi tunanin cewa wani abu ba ne, saboda yanayi na ne kawai," in ji ta. "Ina da 'ya'ya, ina da miji na shekaru da dama kuma sun yi tunanin cewa ina da matukar juriya ne."

Sauyin kwayoyin halittar na nufin cewa abubuwan al'ajabi ba su dadewa suna damunta.

"Abubuwa na sosa min zuciya kamar yadda kowa ke ji, idan abubuwa marasa kyau suka faru, na kan ji kamar yadda kowa zai ji," in ji ta. “Amma cikin kankanin lokaci zan fara tunanin ko akwai matakin da zan dauka don in manta da shi".

Farfesa Cox na sa ran cewa sakamakon binciken zai bayar da damar gudanar da sabbin bincike kan magunguna don taimakawa tare da kula jin zafi, warkar da raunuka da kuma lafiyar kwakwalwa.

Source: BBC