BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Matar da rashin imani ya sa ta yi wa babbar ƙawarta kisan gilla

30173633 Jemma Mitchell

Sun, 6 Nov 2022 Source: BBC

Me zai sanya mace kashe abokiyarta da daddatsa gawarta tare kuma da sanya ta cikin akwati har na tsawon makwanni biyu, daga baya kuma ta jefar da ita a wani wuri mai nisan kilomita 200? Ga Jemma Mitchell, wannan abu mai sauki ne. ''Mitchell mace ce mai kisa, kuma ba ta da imani. Kuɗi ne yake sanya ta aikata hakan. Wannan abin tayar da hankali ne matuƙa'', a cewar Det Ch Insp Jim Eastwood, jami'in ɗan sandan birnin Landan. Wannan labarin wata abota ce da ta faro daga wata majami'a, inda ta kuma kawo karshe lokacin da ɗaya daga cikin abokan ta mutu, yayin da ɗayar kuma ke rayuwa a ɗaure. Wasu iyalai ne da suka je hutawa a bakin teku, suka fara cin karo da gawar matar wacce ƙawarta ta kashe ta. An ɗauki tsawon kwanaki 16 ba a ga Mee Kuen Chong ba, wacce aka fi sani da Deborah haifaffiyar ƙasar Malaysia. A yanzu an gano gawar matar mai shekara 67, kwanaki ƙalilan bayan faruwar lamarin a wani wuri da ke Salcombe a Devon mai nisan kilomita 200 daga gidanta da ke arewa maso yammacin Landan. Shekara ɗaya bayan faruwar lamarin, kotu ta fara zaman jin bahasi na yadda aka kashe Deborah wanda mutane ba za su taɓa mantawa ba. Deanna Heer KC, shi ne babban mai shigar da ƙara da ke jagorantar shari'ar. Abin takaici ne: ''Jemma Mitchell ta ci zarafi tare kuma da kashe ƙawarta sannan ta ɗauki gawarta zuwa Salcombe a cikin ƙananan akwatuna, inda ta yi ƙoƙarin jefar da ita a can. Bayan zaman kotu na tsawon makonni biyu, Mitchell ta saurari batun da ake zargin ta da shi, yayin da iyalan Miss Chong kuma suka kalla ta hoton bidiyo daga Malaysia. Mista Heer KC ya fada wa kwamitin lauyoyi masu yanke hukunci cewa a ƙarara take cewa matar ta aikata laifin wanda kuma kuɗi ne ya ingiza ta''. Mitchell ta fito daga iyalai masu kuɗi, inda ta yi karatu a makarantar kuɗi, inda mahaifiyarta kuma ke aiki a ofishin harkokin waje. Ta mallaki kadarori a Australiya wanda ya kasance wurin da aka haife ta, inda gidansu da ke birnin Landan yake a yankin da ba a sayar da gidaje kan kuɗi ƙasa da £1m. Saƙonnin kar-ta-kwana daga wajen Miss Chong sun nuna cewa gidan Mitchell zai kai £4m. Gidan na bukatar a sake gyara shi. Ɗakunan sun cika da ƙura wanda hakan ya sanya da wuya a iya shiga ciki, kamar yadda Mista Heer KC ya faɗa wa kwamitin lauyoyi. ''Akwai akwatuna da firiji cike da abinci da tsoffin katifu da kuma kayan gine-gine a ko-ina. Ɗakin dafa abincin ma cike yake da datti da abinci da ya lalace, inda takardu suka rufe kan abincin,'' a cewar Miss Heer KC. ''Bayan gidan ma a lalace yake, inda yake buƙatar gyara. Gidan ba shi da kyawun gani. Ana aikin gyara bene na biyu na gidan. Kotun ta ce ta ji cewa Miss Chong ta bai wa Mitchell £200,000 domin aikin gyara gidanta, amma daga baya ta ki amincewa da hakan. Jim kadan aka neme ta aka rasa. Dukkan matan sun kasance kiristoci masu bauta ta gaske, inda suke haɗuwa a coci a koda-yaushe a wuraren watan Agustan 2020. Mitchell ta yi amfani da wata manhajar yanar gizo ta kiristoci, inda Miss Chong ta kasance ita ma tana mu'amala da shafin wajen wallafa saƙonnin bauta na addinin kirista. Ba a dai san me ya janyo matan biyu haɗuwa ba, sai dai miss Chong ta kasance mace mai lalurar ƙwaƙwalwa, inda Mitchell da ke da digiri a fannin magunguna masu warkas da ƙasusuwan jiki. Ta bai wa ƙawarta shawara kan matsalar ta. An fi sanin Miss Chong a matsayin mutuniyar kirki, inda take taimaka wa marasa galihu da ke buƙatar taimako. Bisa dukkan alamu, matan biyu sun kasance cikin ƙwance mai kyau, sai dai bayan gano gawar Miss Chong, jami'ai sun yi ta neman hotunan bidiyo domin gano wanda ya kashe ta. Daga baya ne dai bayanai suka fara fitowa kan wadda ta kashe ta. Jami'in ɗan sandan birnin Landan, Det Ch Insp Eastwood, ya ce akwai hujjoji da dama da suka nuna cewa Mitchell ce ta aikata kisan. "Hotunan bidiyo sun nuna Mitchell na kai wa da kawowa a gidan Deborah ranar da ta ɓace. Akwai kuma wasu hotuna da suka nuna Mitchell lokacin da ta yi balaguro zuwa Devon. ''Mun samu nasarar gano ƙananan akwati wanda muke kyautata zaton cewa da shi Mitchell ta yi amfani wajen zuwa jefar da gawar kawarta a titin Chaplin a wajen shakatawa na Brondesbury. ''Mun iya gano cewa Mitchell ta bar wayar ta a gida, inda ta yi amfani da wayar kawarta da ta kashe lokacin da ta je jefar da gawarta a Devon,'' a cewar Eastwood. Ya kuma ce sun samu ƙwararan shaidu a gidanta da suka nuna cewa ita ta aikata kisan, inda muka samu bayanai daga wajen takardu na kuɗi wanda Mitchell ta ɗauka daga gidan Deborah a ranar 11 ga watan Yuni. Lauya mai shigar da ƙara ya fada wa kwamitin lauyoyi cewa Mitchell ta ɗauki kuɗaɗen ne domin amfani da su. Har ila yau, jami'in ɗan sandan ya kwatanta kisan da aka yi wa Miss Chong a matsayin abin takaici da kuma mai tayar da hankali. Kotun dai ta fi mayar da hankali kan ƙananan akwatuna masu shuɗin launi da aka gano Mitchell a ja kan titunan birnin. Mai shigar da ƙaran ya ce ta ɗauki akwatuna ne zuwa gidan Miss Chong da nufin kashe ta da kuma sanya gawarta cikinsu. Kwamitin lauyoyin sun bayyana cewa lokacin da Mitchell ta bar gidan ƙawarta, akwatuna suna da nauyi waɗanda kuma ke da wahala mutum ya ɗauka''. Makonni biyu bayan faruwar lamarin, Mitchell ta yi amfani da sunan bogi da kuma wayar ƙawarta da ta kashe ta kuma samu mota ta sanya akwatin tare da tafiya da shi zuwa Devon. Lauyoyi sun ce ta yi tafiyar ne domin zuwa jefar da gawar miss Chong. "Babu wanda zai iya aikata irin wannan kisan kai idan ba mara imani ba." Abin da Mitchell ta yi na tafiya yin soyayya da wani da ta haɗu da shi a yanar gizo bayan kisan Miss Chong, ya ƙara nuna cewa ba ta da imani saboda ko damuwa da abin ba ta yi ba. Wani bakanike ne ya fara gano irin ɗabi'un da Mitchell ke yi akwai wani abu a ƙasa lokacin da yaje gyara mata tayar mota. Ya kuma jiyo wari na fita daga cikin motar, inda ta ki yarda bakaniken ya buɗe bayan motar ta domin ɗauko tayar da zai canja mata. Mitchell dai ta ƙi bayar da shaida a gaban kotu. Tun bayan kama ta a ranar 6 ga watan Yulin 2021, ta ki cewa uffan game da batun kawo yanzu. Kotun ta gano cewa Mitchell ta kammala karatu daga Kings College da ke birnin Landan a fannin kimiyar ɗan adam. Tana kuma da kwarewa kan yadda za a yanka bangaren jikin dan adam. Kamar cire kai, duk da cewa ba a san haƙiƙanin abin da ya sanya ta yi hakan ba. Ta kuma yi aiki a matsayin masaniyar magungunan warkas da kasusuwan jiki a Australiya na tsawon shekara bakwai kafin ta koma Birtaniya a 2015, inda ta zauna da mahaifiyarta da kuma ƙanwarta, a wani zama mai cike da sarƙaƙiya. Mitchell ita kaɗai ta san me ya faru a gidan Miss Chong da ke titin Chaplin a ranar da ta kashe ta a watan Yunin 2021. Det Ch Insp Eastwood : ''ya ce sai dai mu yayata abin da Mitchell ta yi da kuma abin da ta shirya. ''Mitchell kaɗai ta san cewa ta daddatsa gawar Deborah a wancan lokaci. "Bayan daddatsa gawar Deborah, Mitchell ta yi fargabar cewa za a iya gano abin da ta aikata - wanda hakan ne ma ya sa ta ɗauki gawar zuwa yankin Salcombe da ke Devon. "Sai dai, abin ya fito ƙarara shi ne bayan Mitchell ta ga damar samun kuɗaɗen ya ɓace mata - kawai sai ta yanke shawarar far wa ƙawarta wadde mutane suka shaide ta a matsayin mutuniyar kirki tare kuma da kashe ta domin cikar burinta na samun kuɗaɗe, wannan babban laifi ne,''. Kotun dai ta samu Mitchell da laifin kisan kai, sai dai ta musanta hakan, inda yanzu ake jiran yanke mata hukunci.

Source: BBC