Menu

Matasan Brazil sun ci 9-0 sun kai hari sau 81 a gasar kofin duniya

11291093 Hoton alama

Wed, 15 Nov 2023 Source: BBC

Brazil ta doke New Caledonia 9-0 da kai hare-hare 81 a rukuni na uku a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17.

Hakan na nufin mai riƙe da kofin, wato Brazil kan kai hari raga a duk daƙiƙa 75, wadda ta ci ƙwalo uku kan hutu daga baya ta ci sauran a zagaye na biyu.

Waɗanda suka ci mata ƙwallayen har da Simplício Rocha, wanda ya ci uku rigis da Almeida de Oliveira Gonçalves da Sousa Santos da Nogueira da shi ma ya zura uku a raga da De Oliveira Nunes dos Reis da kuma Cunha.

Tawagar matasan Sifaniya ce ke da tarihin ɗura ƙwallo 13-0 a ragar New Zealand a gasar 1997.

Ranar Asabar Ingila ta sharara 10-0 a ragar New Caledonia a dai karawar rukuni na uku a Jakarta da kai hare-hare 39.

Brazil wadda Iran ta doke ta 3-2 a wasan farko a rukuni na ukun a gasar da ake yi a Indonesia ta kai hari kaso 28 cikin 100 da ya nufi raga a wasa da New Caledonia.

Yayin da kaso 33 cikin 100 shi ne bai nufi raga ba da kuma kwallo 25 da golan New Caledonia ya hana shiga raga.

Source: BBC