Menu

Matsalar rashin tsaro ta fara sauƙi a jihar Katsina

90455695 Hoton alama

Mon, 1 Jan 2024 Source: BBC

Alamu na nuna cewa an fara samun sauƙin matsalar tsaro a sassan da ta yi ƙamari a jihar Katsina ta Najeriya inda ake samun labarin cewa harkokin zamantakewa da na tattalin arziƙi sun fara farfadowa a yankuna da dama da matsalar ta yi ƙamari a baya.

Bayanai da ake samu daga mazauna yankunan da matsalar hare-haren 'yan bindiga ta addaba a jihar, sun ce an fara samun sauƙi, sakamakon matakan da ake ganin gwamnatin jihar da jami'an tsaro ke ɗauka kan lamarin.

Wani mazaunin yankin Dandume, Nasiru Garba ya yaba wa yunƙurin da hukumomi ke yi na daƙile matsalar rashin tsaron, inda ya ce, 'An kawar da kusan kashi 80 cikin 100 na matsalar tsaro, an farfaɗo da kasuwanci, an sami walwala, inda ba a iya zuwa yanzu ana zuwa, kuma kowa ya sami kai amfanin gonarsa gida'.

Ya ƙara da yin kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi wurin magance matsalar baki ɗaya.

A yankin ƙaramar hukumar Faskari, mazauna yankin sun yi maraba da sauƙin da aka samu daga hare-haren ƴan bindigan.

Wani mazaunin yankin, Hamza Dahiru Inuwa ya shaida wa BBC cewa duk da cewa lamarin ya yi sauƙi, akan sami aukuwar hare-haren jifa-jifa.

'Kwanankin baya gaskiya an sami sauƙi sosai amma a cikin kwanakin nan an sami mutane huɗu da suka mutu sakamkon wani hari da ƴan bindiga suka kawo wannan yankin,' in ji shi

Ya shawarci jami'an tsaro da su yi aiki tare da ƙungiyoyin ƴan sa-kai a yankin.

Dangane da hanyoyin da ake bi, har aka kai ga fara samun wannan sauƙi kuwa, sai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsana, Dakta Nasiru Mu'azu ya ce: 'Ɗaya daga cikin matakan da aka ɗauka shi ne na binciko mutanen gari masu taimaka wa waɗannan 'yan bindigan, muna nan ba dare ba rana muna ta zaƙulo su, duk inda suke sai mun nemo su kuma sai mun yi maganinsu. Dole su bar al'umma su zauna lafiya'.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da za su tabbatar da cewa lamarin bai sake taɓarɓarewa kamar yadda ya faru a baya ba.

Masu lura da lamuran tsaro dai na ganin ya kamata sauran jihohin da ke fama da irin wannan matsala ta 'yan bindiga, su bi mataki na bai-daya wajen koyi da salon jihar Katsina na shawo kan matsalar.

Source: BBC