Menu

Matsalar tsaro ta jefa mazauna kan iyakokin Najeriya da Nijar tsaka mai wuya

Nijar macobci ne ga Najeriya, Mali, Libya, Algeria, Benin da Burkina Faso

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

Matsalar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya ba baƙuwa ba ce, kamar dai yadda take a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Sai dai ko a arewa maso gabashi akan samun lokacin da abubuwa ke sassautawa, har ma a riƙa mayar da mazauna ƙauyuka garuruwansu da suka baro.

Lamarin ya sha bamban da abubuwa ke faruwa a yankin arewa maso yammaci musamman ma a ƙananan hukumomi da ƙauyukan da ke kan iyakokin Najeriya da Nijar.

Cikin wata hira da BBC ta yi da Honarabil Sani Alhaji Yakubu Ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Gudu da Tangaza ya bayyana yadda matsalar ke ci gaba da ƙazanta.

Ya ce ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza da Binji da kuma Gwadabawa da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya dukkansu matsalar satar shanu da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa ta addabe su.

Kan haka nema ya gabatar da wata buƙata gaban majalisar wakilan tarayya ta neman hukumomin tarayya su kai musu dauki.

"Babu yadda za a yi ka yawata ƙauyukan kananan hukumomin Tangaza da Gudu da Binji da Gwadabawa cikin kwanciyar hankali.

"Matsalar ta yi ƙamarin da mutane da yawa sun haƙura da inda aka haife su sun sauya wuri," in ji Sani Alhaji Yakubu.

'Dajin Tsauna da na Kuyan Bana ne mafakar ɓata garin'

Dan majalisar ya ce abin da ya sanya yankunan da yake wakilta suke fama da wannan matsala shi ne manyan dazuka da ake da su, waɗanda suka zamar wa waɗannan ɓata gari mafaka.

"Dajin Tsauna shi ne ya taso daga Raka zuwa Gwadabawa har Illela sai da ya tuƙe ga Nijar.

"Akwai dajin Kuyan Bana wanda ke cikin ƙaramar Hukumar Gudu ya tuƙe ga Nijar.

"Duka 'yan ta'addar da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar da namu na cikin gida ba su da wata mafaka da ta wuce wannan wuri," in ji Honarabil Sani Alhaji.

A cewarsa buƙatarsa ta yi daidai da alƙawarin da gwamnatin Tarayya ta yi na ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Ya ƙara da cewa ƙudurinsu shi ne gwamnatin Tarayya ta ba da isassun makamai da jami'an sojin ƙasa da na sama domin a shiga a yaƙi wannan daji.

Ka zalika ta bayar da jami'an 'yan sanda da na farin kaya domin zaluƙo masu bai wa waɗan nan 'yan bindiga bayanai kan halin da yankunan ke ciki.

'Masu iƙirarin jihadi daga Libya da Mali ma na zuwa yankin'

Ɗan majalisar wakilan ya tabbatar da cewa masu iƙirarin jihadi daga ƙasashen Libya da Mali na zuwa wani yankin da ake cewa Lakurawa.

Sai dai ya ce suna zuwa ne lokaci zuwa lokaci domin haka ba kasafai aka fiye ganinsu ba a yankin.

Buƙata ce irin ta neman mafaka ke kai su yankin da zarar sun kammala abin da suke yi sai su fice, in ji ɗan majalisar.

"A baya suna daɗewa su yi ta wa'azi su kai hari kan waɗanda suka ƙi amincewa da da'awarsu, amma yanzu sai dai su zo kwana biyu zuwa mako guda su ta fi a matsayin neman mafaka,".

Honarabil ya ce dalilin da ya janyo mutanen yankin da yake wakilta ke cikin wannan hali shi ne, sun ƙi amincewa su bayar da kai bori ya hau.

Sun ƙi amincewa da sharaɗin biyan haraji, ko kuma su ta fi su bar ƙauyukan da suke ƙarfi da yaji.

Matsalar dai na neman gagarar kwandila, kuma da wannan shige da fice da ake samu daga mayaƙan kasahen da ke makwabtaka masu iƙirarin jihadi, hakan na nufin matsalar za ta iya munana a nan gaba.

Source: BBC