Menu

Matsayar gwamnatin Najeriya kan ce-ce-ku-cen haramta cin taliyar 'Indomie'

Hoton alama | Indomie

Tue, 2 May 2023 Source: BBC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya, Nafdac, ta ce za a iya cin taliyar indomie a ƙasar saboda ba ta ɗauke da sinadarin haddasa cutar kansa.

Shugabar hukumar Nafdac, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da BBC, inda ta ce taliyar ta indomie da ta sahhale a ci, a ƙasar ake samar da ita.

Farfesa Adeyeye ta ce a shekarun baya, gwamnatin tarayya ta haramta shigo da indomie cikin ƙasar domin karfafa gwiwar masu samar da ita a ƙasar.

An yi ta samun rahotanni mabanbanta cewa taliyar indomie mai ɗanɗanon kaza da Taiwan da Malaysia ke samarwa, tana ɗauke da sinadarin Ethylene Oxide da ke haddasa cutar kansa.

Sai dai, Nafdac ta ce indomie da ake samarwa a cikin ƙasar ba ta da wata alaƙa da ta Taiwan da kuma Malaysia.

'Nafdac na gudanar da bincike kan taliyar indomie da dangoginta'

Nafdac ta ce ta fara gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie da kuma cikin kasuwannin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da Taiwan da Malaysia suka ce wata taliya mai ɗanɗanon kaza na ɗauke da sinadarin da zai iya janyo cutar kansa.

Nafdac ta ce babu irin nau'in taliyar ta indomie a cikin kasuwannin Najeriya, inda ta ce za su yi gwaji don gano ko wasu ɓata-gari sun shigo da ita cikin ƙasar.

Farfesa Adeyeye ta ce taliyar indomie na cikin abubuwan da hukumar kwastam ta haramta shigo da su ƙasar.

Batun sinadari mai jawo cutar kansa da aka ruwaito cewa indomie na ɗauke da shi ya janyo fargaba kan ingancin abinci a duniya ciki har da Najeriya ganin cewa indomie na cikin abubuwan da ake ci kodayaushe a ƙasar.

Me ya faru a Taiwan da Malaysia?

An fara nuna fargaba kan inagancin taliyar indomie ne bayan da sashin kula da lafiya a yankin Taiwan ya fito ya sanar cewa ya gano wasu sinadarai guda biyu na ethylene oxide cikin nau'i biyu na taliyar indomie.

Cikin dangogin indomie da aka gano sinadaran sun haɗa da mai ɗanɗanon kaza, wanda suka tabbatar da hakan bayan gudanar da bincike.

Hukumomi sun ce sinadarin ethylene oxide da ke cikin taliyar ta indomie na cikin rashin kyawun tsari.

“Hukumar lafiya a birnin Taipei na Taiwan na tunatar da mutane cewa ta gano sinadarin ethylene oxide mai haddasa cutar kansa a cikin indomie.

Saboda haka, ma'aikatar lafiya ta Malaysia ta ce sun yi gwaje-gwaje a kan taliyar indomie guda 36 na kamfanoni daban-daban tun daga 2022, kuma sun gano cewa samfura 11 na ɗauke da sinadarin ethylene oxide.

Sai dai Malaysia ta ce ba ta ɗauki matakin tilastawa tare kuma da kiran nau'iukan da abin ya shafa ba na zuwa gabanta.

Ƙasashen biyu sun bayar da umarnin cewa ƴan kasuwar su fitar da taliyar ta indomie cikin shagunansu nan take.

Me ya sa Najeriya ta nuna damuwa?

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe da ake yawan cin indomie a faɗin duniya.

Hakan ne ya sa hukumar Nafdac ta ɗauki matsaya kan damuwa da ake nunawa kan ingancin taliyar ta indomie da ta sanya fargaba cikin zukatan ƴan Najeriya sama da miliyan ɗaya ciki har da yara waɗanda galibi suke son cin indomie.

Akwai bukatar indomie a cikin sassan Najeriya da dama, duk da cewa akwai kamfanonin samar da shi da yawa a cikin ƙasar.

Source: BBC