Menu

Matuƙar haɗin kan da muka ba Buhari ya zame wa Najeriya matsala - Ndume

Ali Ndume Sanata Ali Ndume

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Yayin da majalisar dattijan Najeriya ta tara ke shirin zaman bankwana, bayan ƙarewar wa'adinta, masu ruwa da tsaki na ci gaba da tsokaci a kan nasarori da ƙalubalen da ta fuskanta a cikin shekara huɗu.

Wani jigo a majalisar ya ce yawan haɗin kan da suka bai wa gwamnatin Buhari ya sanya har sun riƙa kau da kai ga matsalolin cin hanci da rashawa.

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai yayin wata hira da BBC kafin rufe majalisa ta tara a ranar Asabar, ya ce duk da yake akwai ɓangarorin da suka yi rawar gani sosai, amma akwai abubuwan da ya kamata su ƙalubalanci gwamnatin Muhammadu Buhari.

A cewarsa, rashin taka burki ga wasu buƙatun gwamnati waɗanda ga dukkan alamu akwai yiwuwar zarmiya, bai taimaki Najeriya ba.

"Ba a taɓa samun majalisar da ta bai wa ɓangaren zartarwa haɗin kai kamar yadda majalisa ta tara ta bayar ba".

"Duk da cewa, ya kamata mu ba da hadin kai (ga ɓangaren zartarwa) amma mun wuce gona da iri, kuma ya zamar wa ƙasa matsala musamman a fannin basukan da gwamnati ta yi ta karɓowa," in ji Sanata Ndume.

Ya dai soki lamirin majalisa ta tara a kan rashin yin bincike da bin diddigi da kuma tantance yadda ake amfani da basukan da gwamnatin Buhari ta karɓo, da kuma tasirinsu ga al'ummar ƙasar.

'Ba mu yi dokar ƙarfafa yaƙi da cin hanci ba'

Ɗan majalisar wanda ya taɓa zama shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai ya ce ɗaya daga cikin manyan alƙawurran da gwamnatinsu ta zo da su kan mulki, shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa, amma kai tsaye ba su ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki da ya nuna da gaske suke yi ba.

"Abin da muka zo da shi a gwamnatance shi ne cewa za mu yaƙi cin hanci da rashawa kai tsaye, sai dai ba a yi wata doka da za ta nuna haka ba," Ndume ya ce.

Ya ce lamarin gazawar majalisa ce.

A cewarsa dukkansu suna da alhaki a wannan gazawa a matsayinsu na jagorori a majalisa ta tara.

Sanata Ali Ndume ya nuna cewa ba su yi aikinsu na bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa ba. "Kaman yadda na ce an samu haɗin kai da gwamnati, amma an je an wuce gona da iri".

"A cikin gwamnatin an yi aiki, amma ɓarnan da aka yi, in ka kwatanta shi da aikin da aka yi, to sai ka yi mamaki anya kuwa an samu wata riba?, Cewar ɗan majalisar.

Ya ce dole a matsayinsu na sanatoci a majalisa ta tara, su karɓi alhakin gazawar da aka samu a gwamnatin da ta wuce. Ko da yake, ya ce majalisarsu ta cimma ɗumbin nasarori a tsawon shekara huɗu.

Ali Ndume ya kuma ce sun yi faɗa da ɓangaren zartarwa kimanin sau biyu ko uku, amma abin takaici ba su cimma wata nasara ba a kan ƙudurinsu.

'Bashin da aka ciyo ya zame wa Najeriya alaƙaƙai'

Sanata Ndume ya ce haɗin kan da suka bayar ga wasu manufofin gwamnatin da ta wuce kamar basukan da ta yi ta karɓowa sun zame wa najeriya alaƙaƙai.

Ya ce ba su gudanar da binciken da ya dace sosai ba, sannan ba su yi nazarin amfanin karɓo basukan ba. Haka zalika ba su tantance amfanin basukan da aka karɓa a baya ba, da yadda za a biya kuɗin da aka ciyo ba, da kuma abubuwan da za su biyo baya."

An dai ta yi ta sukar gwamnatin Buhari da jefa Najeriya cikin ƙangin ɗumbin bashin da za ta shafe tsawon shekaru kafin ta iya biya.

Gwamnatin ta dai karɓo basukan ne a ciki da wajen ƙasar.

Sai dai ta riƙa kare matakin da cewa abu ne da ya zama dole saboda matsalolin ƙarancin kuɗin shiga da annobar korona da kuma karayar tattalin arziƙi har sau biyu da ƙasar ta shiga a tsakanin 2019 zuwa 2023.

Wani muhimmin aiki na majalisar shi ne sa-ido a kan ayyukan ma'aikatu da hukumomin gwamnati, don tabbatar da ganin suna amfani da kuɗaɗen da aka amince musu wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata, amma Ndume ya ce ta wannan bangaren ma, sun gaza.

"Mu aikinmu da ma don komai ya yi kyau ne, ta tafi daidai, to bai yi kyawun ba"

Ndume wanda ke cikin 'yan majalisar da aka sake zaɓa zuwa majalisa ta goma da za a rantsar nan gaba cikin makon gobe, ya kuma ce yana goyon bayan a rushe tsarin majalisa biyu.

Source: BBC