BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Mbappe ya zama kan gaba a ci wa PSG kwallaye a tarihi

64575392 Kylian Mbappe

Sun, 16 Apr 2023 Source: BBC

Paris St Germain ta doke Lens 3-1 a wasan mako na 31 a gasar Ligue 1 da suka fafata ranar Asabar.

Kylian Mbappe ne ya fara cin kwallo kuma na 139 a wasa 169 a kungiyar, kenan ya zarta Edison Cavani mai rike da bajinta a baya.

Lens ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Salis Abdul Samed jan kati minti 19 da take leda.

Sauran da suka ci wa PSG kwallayen sun hada da Lionel Messi da kuma Vitinha, yayin da Lens ta zare daya a bugun fenariti ta hannun Przemyslaw Frankowski.

PSG mai fatan lashe Ligue 1 na 11 tana ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Faransa ta bana da maki 72.

Lens mai maki 63 ce ta biyu, sai Marseille ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Lens.

Paris St Germain za ta ziyarci Angers ranar Juma'a 21 ga watan Afirilu, domin buga wasan mako na 32 a Ligue 1.

Source: BBC