Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ta shirya tsaf domin kammala zaɓukan da suka rage, na gwamnoni da 'yan majalisun tarayyar da kuma na jihohi.
Cikin wata tattaunawa da BBC, jami'ar INEC, Zainab Aminu Abubakar ta ce an kai mafi yawan kayan da ake buƙata zuwa ƙananan hukumomi a ranar Juma'a, kuma za a dangana da su gundumomin da za a yi zaɓen kafin wayewar garin Asabar.
"Muna son fara duk zaɓukan da ba a kai ga samun wanda ya yi nasara ba, da ƙarfe takwas na safe, ba ma son fara ko ɗaya a makare," in ji Malama Zainab.
Cikin zaɓukan da za su ja hankali akwai na gwamna a jihar Adamawa, wanda za a fafata tsakanin gwamna mai ci Ahmadu Umaru Fintiri da Hajiya Aisha Dahiru Binani.
Akwai zaɓen Jihar Kebbi wanda shi ma ba a kammala ba.
Haka nan kuma za a gudanar da zaɓen sanatoci a mazaɓu daban-daban a faɗin ƙasar, waɗanda suka haɗa da.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu a wani jawabi da ya yi, ya ce jam'iyyu takwas ne suka samar da sanatoci a zaɓen da ya gabata.
Jam'iyyun su ne APC, PDP, APGA, SDP, Labour, NNPP, ADC da YPP.