Fafatawa ta yi tsanani a zagayen asibiti mafi girma a Zirin Gaza na Al-Shifa a 'yan kwanakin nan, inda ƙarancin fetur ke hana kula da marasa lafiya.
A ranar Talata da dare dakarun Isra'ila kusan 100 da tankokin yaƙinsu suka kutsa cikin asibitin, suna masu cewa bayanan sirri sun nuna cewa akwai mayaƙan Hamas a wani ɓangare.
Wasu rahotonni na cewa sun karɓe iko da asibitin zuwa safiyar Laraba, inda suka tara mutanen da ke fakewa a farfajiyar asibitin a wuri guda tare da bincikar wasu daga cikinsu.
Kazalika, shaidu da ke cikin asibitin na Al-Shifa sun faɗa wa wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abu Alouf cewa sojojin na bincikawa ɗaƙi-ɗaki, hawa-hawa na kowane bene suna yi wa duk wanda suka gani tambayoyi, ciki har da marasa lafiya, bisa rakiyar likitoci da kuma masu magana da Larabci.
Kafin samamen na Talata, wakilin Sashen Larabci na BBC, Ethar Shalaby, ya yi magana da shugaban sibitin da kuma manyan likitocin Al-Shifa don amsa wasu daga cikin tambayoyin da aka fi yi game da halin da ake ciki.
Makeken ƙabari
Shugaban sashen tiyatar ƙashi, Dr Adnan al-Bursh, ya faɗa wa BBC cewa sun yanke shawarar rage yaɗuwar cutuka ta hanyar binne gawa 120 a farfajiyar asibitin cikin wani makeken ƙabari.
Dr al-Bursch ya ce sun sake kwashe gawa 80 daga mutuwaren asibitin kuma suka binne su a wani babban ƙabarin. Ya ƙara da cewa a cikin ginin asibitin suka haƙa ramukan.
A ina Asibitin Al-Shifa yake?
Asibitin Al-Shifa, wanda ake ganin shi ne mafi girma a Gaza, yana unguwar Rimal ne da ke Birnin Gaza.
Asibitin, wanda ke da gado 700, yana da ɓangarori biyar:
Ɓangaren kula da lafiyar mata, wanda ya ƙunshi ɗakunan karɓar haihuwa;
Wurin tiyata na musamman, wanda ya ƙunshi sashen kulawa akai-akai (ICU);
Babban sashen tiyata da lafiyar ƙashi;
Sashen gashi da lafiyar cikin jiki
Sashen mulki, wanda ya ƙunshi wurin ganin likita, da ɗkunan gwaji, da kuma wurin ajiyar jini.
Babban daraktan asibitin, Dr Muhammad Abu Salamiya, ya ce a lokutan kwanciyar hankali ana kwatanta asibitn a matsayin mafi kyawu a Gaza.
Bugu da ƙari, asibitin koyarwa ne da aka sani har a ƙasashen waje.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗi a ranar 13 ga watan Nuwamba cewa Asibitin Al-Shifa ya kusa zama "maƙabarta" saboda gawarwakin da ke taruwa a ciki da wajensa.
An yi fafatawa tsakanin dakarun Isra'ila da na Hamas a kusa da asibitin a kwanan nan, yayin da ƙarancin man fetur ke shafar kula da marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni.
Wa ke ɗaukar nauyin Asibitin Al-Shifa?
Ma'aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas da ke kula da Zirin Gaza ce ke gudanar da asibitin.
Marasa lafiya nawa ne ke jinya yanzu haka a Al-Shifa?
A cewar Dr Muhammad Abu Salamiya, adadin na sauyawa a kowace rana.
A ranar 13 ga watan Nuwamba, an yi ƙiyasin adadin ya kai 650, ciki har da masu jinyar ƙoda, da jariran da ke cikin kwalaba 36, da marasa lafiyar da ke buƙatar kulawa akai-akai 26, in ji shi.
Akwai kuma ma'aikatan lafiya kusan 700 a asibitin.
Sai da aka kwashe marasa lafiya daga sashe biyu na asibitin zuwa sauran sassa uku, a cewar likitoci.
Adadin mutanen da aka kora daga gidajensu kuma suke neman mafaka a asibitin sun kai 5,000, kamar yadda Dr Abu Salamiya ya faɗa wa BBC.
Tun daga kusan mako ɗaya bayan kai harin ranar 7 ga watan Oktoba dubban mutane suka fara neman mafaka a asibitin, inda a hankali adadin ya dinga ƙaruwa zuwa kusan 60,000, in ji shugaban.
Amma adadin masu neman mafakar ya ragu sosai tun bayan fara kai wa asibitin hari a 'yan kwanakin nan, kodayake dai wasu dubbai na nan har yanzu.
"Wasu daga cikinsu [marasa lafiyar] sun gudu daga asibitin, kuma aka kashe su a kan hanyarsu ta zuwa kudancin Gaza ko kuma wasu gidan ɓuyan a makarantu," in ji Dr Abu Salamiya.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda suka bar asibitin an harbe su ne mita 200 kawai daga asibitin kuma dole suka koma don neman magani.
Da aka tambaye shi ko ina za su je, ya faɗa wa BBC cewa: "Za su mutu idan aka ƙyale su a haka. Ba zai yiwu a ƙyale su haka ba tare da kulawa ba.
"Muna neman a kwashe mu daga wannan asibitin, mu da marasa lafiya," a cewarsa.
Wane hali ake ciki game da man fetur a asibitin?
Dr Abu Salamiya da sauran likitocin asibitin sun faɗa wa BBC cewa babu man fetur, kuma suna dogaro ne kan na ko-ta-kwana, wanda ake amfani da shi kawai idan "ya zama dole".
A yammacin ranar 12 ga wana Oktoba, kakakin rundunar sojan Isra'ila Daniel Hagari ya ce sun bar lita 300 ta man fetur a kusa da asibitin da dare, amma Hamas "na ta matsa wa asibitin kada su karɓa".
Dr Abu Salamiya ya ce ba wai "ƙin karɓar man suka yi ba" - duk da cewa zai iya ba su wuta ne na minti 30 kacal.
Ya ƙara da cewa bai son ya jefa rayuwar ma'aikatansa cikin haɗari ta hanyar karɓar mai "a filin yaƙi kuma da tsakar dare".
Asibitin na buƙatar litar mai aƙalla 10,000 a kullum, in ji shi.
Ko mutane sun samu damar guduwa daga Asibitin Al-Shifa?
Mutane da daa na tambaya a intanet cewa: "Me ya sa mutane ba za su bar asibitin ba kawai?"
Tun da farko kakakin sojan Isra'ila, Daniel Hagari, ya ce "sun buɗe wasu hanyoyi" daga asibitin zuwa kudancin Gaza kuma "suna magan da hukumomi don kwashe marasa lafiya da waɗanda aka jikkata".
Ya ƙara da cewa Isra'ila za ta taimaka wajen kwashe jariran da ke jinya a asibitin.
Sai dai kuma likitocin asibitin sun ce hakan ba zai yiwu ba a irin yanayin da ake ciki.
Shugaban sashen tiyatar ƙashi, Dr Adnan al-Bursh, ya ce an yi wa asibitin ƙawanya tsawon kwana huɗu kuma mutane da yawa a tsorace suke ba za su iya fita ba.
Ya faɗa wa BBC: "Na ga tankokin yaƙin Isra'ila ƙasa da nisan mita 100 daga asibitin, kuma jirage marasa matuƙa na ta yawo kusan kodayaushe a saman asibitin."
Saboda wannan, a cewarsa babu wani ma'aikacin lafiya da ya iya fita daga asibitin.
Ana kai wa Al-Shifa hari?
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an sha kai wa asibitin hari a 'yan kwanakin nan, inda aka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawa.
Isra'ila ta musanta kai wa asibitin hari, duk da cewa IDF ta tabbatar da cewa akwai dakarunta a kusa da shi.
IDF na zargin Hamas na amfani da ƙarƙashin asibitin a matsayin ofishin shirya hare-hare, har ma suka fitar da wasu hotunan bidiyo na 3D da ke iƙirarin nuna ofisoshi da ɗakuna a ƙarƙashin ƙasa.
Hamas da shugabannin asibitin sun ƙaryata batun.
Dr Abu Salamiya ya faɗa wa BBC: "Isra'ila ƙarya suke yi. Muna neman MDD, da ƙungiyar Red Cross, da sauran ƙungiyoyin ƙasashen waje su tura tawagoginsu don gudanar da bincike ko akwai wasu mayaƙa a cikin asibitin Al-Shifa.
"Wannan gini ne na farar hula da ke kula da marasa lafiya. A shirye muke duk wanda yake so ya zo ya duba."