BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Me taron ECOWAS zai mayar da hankali a kai a Abuja?

85312810 Shugabannin ƙungiyar ECOWAS a Abuja

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Shugabannin ƙungiyar ECOWAS za su gudanar da taronsu a Abuja babban birnin Najeriya.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan matsalolin da yankin yammacin Afirka ke fuskanta kama daga na juyin mulki da kuma tattalin arziki.

Kazalika batun takunkuman da kungiyar ta kakaba wa Nijar na daga cikin batutuwan da ake sa ran taron zai mayar da hankali a kai.

Taron ECOWAS din da aka yi na karshe ya mayar da hankali ne kan halin da Nijar ta tsinci kanta bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023 wanda ya janyo hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Tuni mataimakiyar sakataren harkokin kasashen Afirka ta yamma Molly Fee, ta isa Najeriya don halartar taron da kuma shiga Tsakani kan rikicin shugabancin Nijar.

Ana kyautata tsammanin Ms Fee, za ta tattauna da shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, da sauran shugabannin kasashen Afirka ta yamma kan yadda Amurka za ta taimaka wajen dawo da mulkin dimokradiyya a Nijar tare da inganta tsaro da zaman lafiya a yankin.

Kungiyar ECOWAS dai ta kakaba wa Nijar takunkumai da dama abin da ya jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin yanayi.

Masana kamar Farfesa Jibrin Ibrahim, na cibiyar ci gaban dimokradiyya da ke Abuja ya shaida wa BBC cewa, taron na da muhimmanci sosai saboda kasashe hudu daga cikin 15 da ke kungiyar ECOWAS din sojoji sun yi juyin Mulki.

A ganinsa dole yanzu ECOWAS ta yi nazari a kan abin da ya kamata ta yi kan matsalar juyin Mulki a tsakanin kasashen, sannan dole ta tabbatar da abin da zata iya yi don ganin an shawo kan sojojin da suka yi juyin Mulki a kan su canja ra’ayi domin a koma kan mulkin dimokradiyya da kuma tabbatar da cewa ba a kara samun juyin Mulki ba a sauran kasashen.

Farfesan ya ce, ba lallai ba ne a yayin taron a cire takunkuman da aka sanyawa Nijar, saboda ECOWAS na cewa,” Idan aka janye takunkuman sojojin za su ga cewa babu abin da zai dame su ko ya ja mu su matsala don haka za su ci gaba da Mulki. Wannan shi ne dalilin da ya sa ECOWAS ba ta son ta janye takunkuman."

Source: BBC