Menu

Me ya sa Birtaniya ke son tura masu neman mafaka zuwa Rwanda?

Rishi Sunak, firaministan Britaniya

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Gwamnatin Birtaniya na son tura masu neman mafaka a ƙasar zuwa Rwanda.

To sai dai shirin haramtacce ne, kamar yadda kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana.

To amma gwamnatin Birtaniya ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukunci a Kotun Kolin ƙasar.

Abin da shirin ya ƙunsa?

Ƙasar Birtaniya na shirin aika masu neman mafaka zuwa kasar Rwanda, za a ba su damar zama a Rwanda a matsayin 'yan gudun hijira.

In kuwa ba haka ba, to sai dai su nemi izinin zama a ƙasar bisa wani dalili na daban, ko neman mafaka ''a wata ƙasar daban.

Gwamnati ta ce matakin zai hana mutane tuɗaɗa zuwa Birtaniya ta ɓarauniyar hanya, ko hanya mai haɗari, kamar amfani da ƙananan jiragen ruwa.

Fiye da mutum 45,700 suka shiga Birtaniya ta irin wannan hanya a shekarar 2022, adadi mafi yawa tun bayan da aka fara tattara irin waɗannan alƙaluman.

Amma a shekarar 2023 yawan ƙananan jiragen ruwa da ke shiga Birtaniya ɗauke da 'yan ci rani na raguwa sannu a hankali.

Kawo yanzu ba a tura ko mutum guda zuwa Rwanda ba.

Da farko an tsara fara jigilar 'yan ci-ranin a cikin watan Yunin 2022, to amma an soke shirin bayan hukuncin kotu.

Abin da kotu ta ce kan matakin

A cikin watan Yunin 2023, kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin da babbar kotun ƙasar ta yanke, wadda a baya ta ce shirin halastacce ne.

Alƙalin kotun ya ce Rwanda ba ƙasa ce da masu neman mafaka za su samu duka abubuwan da suke buƙata domin rayuwa a can ba.

Saboda tsare-tsarenta na masu neman mafaka ya ƙunshi mayar da wasu masu neman mafakar zuwa ƙasashensu na asali, waɗanda watakila su iya fuskantar tuhuma a ƙasashen nasu.

Kotun ta ce matuƙar ba a yi gyara a waɗannan dokokin ba, to matakin tura masu neman mafaka zuwa Rwanda haramtacce ne.

To sai dai hukuncin bai samu sahalewar duka alƙalan kotun ba, domin kuwa biyu ne kawai daga cikin alƙalan kotun uku suka amince da wannan hukunci.

Kungiyar kula da masu neman mafaka ta 'charity Asylum Aid' wadda ta kai gwamnatin Birtaniya gaban kotu ta yi maraba da hukuncin, tana mai cewa ya tabbatar da muhimmancin bin doka da oda.

Firaministan ƙasar Rishi Sunak ya ce bai amince da hukuncin kotun ba, kuma zai nemi damar ɗaukaka ƙara a Kotun Kolin ƙasar.

Yayin da ake ci gaba da shari'a a Kotun Kolin ƙasar, ba za a fara jigilar masu neman mafakar zuwa Rwanda ba.

Mutum nawa za a tura Rwanda?

Gwamnatin Birtaniyar ba ta bayyana adadin mutanen da za ta tura Rwanda ba, to amma a baya ta ce duk mutumin da ya shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba daga ranar ɗaya ga watan Janairun 2022, za a tura shi Rwanda.

A lokacin zaman shari'ar, ƙasar Rwanda ta ce za ta iya ɗaukar ɗawainiyar masu neman mafaka 1,000, kuma ta ce tana iya ɗaukar nauyin sama da haka.

A ƙarkashin shirin, Rwanda ka iya neman Birtaniya ta aika mata wasu daga cikin 'yan gudun hijirarta marasa galihu.

A watan Octoban 2022, kamfanin jirgin sama na Privilege Style da aka tsara zai yi jigilar masu neman mafakan, ya janye kansa daga cikin yarjejeniyar, bayan kiraye-kirayen da ƙungiyoyin da ke fafutikar suka yi.

Haka kuma rahotonni sun ce wasu ƙarin kamfanoni biyu da aka tsara jigilar da su, sun janye daga yarjejeniyar.

Nawa ake tunanin shirin zai laƙume?

Kawo yanzu Birtaniya ta biya gwamnatin Rwanda fam miliyan 140, to sai dai ba ta bayyana ainihin abin da shirin zai laƙume ba.

Gwamnatin Birtaniya ta ce za a kashe wa kowanne mutum guda fan 169,000 domin fitar da shi zuwa Rwanda, fiye da fan 106,000 da gwamnatin Birtaniyar ke kashe wa kowanne ɗaya daga cikinsu.

Fan 169,000 ya kunshi fan 105,000 da za a biya Rwanda kan kowanne mutum guda, tare da kuɗin jirgi fan 22,000 da za a biya wa kowa.

Masu suka na cewa kudin da ake kashe wa masu neman mafakar na zarta kima.

Wane ne mai neman mafaka?

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana 'Mai Neman Mafaka' da cewa shi ne mutumin da ya nemi wajen zama da kariya a wata ƙasa.

Dan gudun Hijira kuwa shi ne mutumin da yaƙi ko muzgunawa suka tilasta masa barin ƙasarsa zuwa wata ƙasar.

Kuma akwai dokokin ƙasa-da-ƙasa da ke kare 'yan gudun hijira. To sai dai kowacce ƙasa na da damar bai wa mai neman mafaka matsayi irin na ɗan gudun hijira.

A shekarar 2022, Birtaniya ta karɓi takardun masu neman mafaka sama da 89,000, adadi mafi yawa cikin shekara 20.

Kuma daga ciki, fiye da mutum 23,000 aka amince da buƙatun nasu na zama a ƙasar a matsayin masu neman mafaka.

Source: BBC