Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Fasaha Ta Wudil da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya (KUST Wudil), ta umarci dukkan ɗalibai mata na makarantar su sanya abaya a ranar Alhamis, inda suka ayyana ranar a matsayin Ranar Abaya.
Wasu ɗaliban makarantar sun tabbatar wa BBC cewa mataimakin shugaban jami'ar mai kula da sha'anin mulki da kuma shugaban tsangayar kula da al'amuran ɗalibai ne da kansu suka sanar da hakan ga ɗaliban.
Wata ɗaliba da ta buƙaci BBC ta sakaya sunanta ta ce "tawagar hukumar makaranta da kanta ta je har hostel don sanar da mu wannan mataki."
Hukumar makarantar ta ɗauki wannan mataki ne bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda wasu ɗalibai maza suke cin zarafin wata ɗalibai da ke sanye da abaya tare da yi mata ature da ihun "mai abaya, mai abaya," al'amarin da ya sa ta muzanta a cewar wasu ɗalibai.
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a makarantar da kuma shafukan sada zumunta da muhawara.
Hukumar KUST dai ta ce za ta ɗauki "mummunan mataki" kan ɗaliban da suka ci zarafin ɗalibar.
Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a ranar Talata, shugaban sashen harkokin ɗalibai ya nemi afuwar ɗalibar sannan ya buƙaci ta shigar da ƙara a hukumance domin neman haƙƙinta.
"Hukumar Kano University of Science and Technology Wudil ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shafukan zumunta game da wata ɗaliba da ɗalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya," a cewar sanarwar.
"Ni shugaban sashen harkokin ɗalibai zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Ɗalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko ɗaukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami'an tsaro."
Sanarwar ta ce abaya ba ta saɓa wa dokar saka tufafi ta jami'ar ba, "saboda haka ɗalibar ba ta karya wata doka ba".
Ranar Abaya
Ranar Abaya da hukumar Jam'iar Wudil ta ayyana za ta zamanto ɗalibai mata sun saka abaya ne don a kawar da tsangawamar da ake yi wa masu sanya ta.
Ɗaliban da BBC ta yi hira da su sun ce a ranar Alhamis ɗalibai da dama sun bi umarnin hukumar makaranta sun sanya dogwayen rigunan.
"Sannan hukumar makaranta ta gaya mana cewa har hotuna na musamman da yammacin Alhamis na masu sanye da abayar.
"Gaskiya mun ji dadin hakan don ba wannan ne karo na farko da aka ci zarafin masu sanye da abaya ba, Allah ne dai Ya taimaka aka yi bidiyon wannan din har ya yaɗu.
"Matakin hukumar makarnta na umartar duk ɗalibai mata su sanya abayar zai yi matuƙar tasiri wajen kawo ƙarshen tsangawamar masu saka ta," a cawar ɗalibar da ba ta so a bayyana sunanta.
Mece ce abaya?
Abaya na nufin doguwar riga irin ta ƙasashen Larabawa da matan Afirka ma ke sanya su a wannan zamani.
Riga ce ko baƙa ko duk launin da mutum ke so, amma doguwa ce har ƙasa mai dogon hannu da kuma mayafin da ake lulluɓe kai har zuwa wuya da shi.
Yawanci a ƙasashe irin Saudiyya da UAE da Qatar da Oman da Kuwait da sauran ƙasashen Larabawa, matansu ba su da wata shiga da ta wuce ta abaya.
A yanzu irin wannan shiga ta zama ruwan dare a Najeriya ta yadda ake shigo da samfuran abaya kala-kala daga ƙasashen waje, masu tsada da masu araha.
Mata da dama sun bayyana cewa tana da sauƙin sha'ani wajen sawa da rashin nauyi da yalwa shi ya sa suka zaɓi sakata a lokuta da dama.
Me ya jawo tashen abaya?
A cikin watan Afrilu lokacin azumin watan Ramadana ne samari a shafukan sada zumunta da muhawara musamman Tuwita suka fara tsokanar ƴan mata da cewa teloli za su yi musu rashin kyautawa ta wajen ƙin kammala musu ɗinkunan sallarsu.
Su kuma ƴan matan sai suka dinga mayar da martani da cewa idan telolin suka "kwabsa" musu sai kawai su suka abaya ranar sallah.
Daga nan ne sai aka ƙirƙiri maudu'in "Wear Abaya On Eid", wato "Ku Saka Abaya Ranar Sallah."
Wannan maudu'i ya shafe kwanaki yana tashe a kafatanin shafukan sada zumunta a Najeriya, musamman ƴan arewacin ƙasar.
Daga baya lamarin ya ɗauki wani salo inda samari suka dinga tsokanar junansu da cewa: "Ko ka saya wa budurwarka abaya?" "Wace irin abaya za ka saya wa budurwarka?" Da sauran kalamai makamantan wannan.
Yayin da su kuma ƴan mata suka dinga tsokanar samarin da cewa: "Idan ba ka sayo a baya a matsayin kyautar sallah ba to za mu ɓata," da sauran su.
Kazalika wata ma'aikaciyar banki ma ta ce "wallahi rannan daga wajen aiki na taso a Kano ranar wata Juma'a da yamma da abaya a jikina, amma sai da na gwammace ban sanya ta ba. Kusan ature yara suka yi min, ana faɗar kalaman da tamkar iskanci na yi na samo rigar," ta faɗa cikin taƙaici.
"Haba jama'a! Don kawai an ga mace ba ta da karsashin tunkarar faɗa a kan titi sai a dinga muzantata? In ji Aisha Lawal wata mazuniyar Kano da BBC ta nemi jin ta bakinta.
"Ta ƙara da cewa gaskiya dole malamai su sake yin wa'azi su kore maganganunsu na farko don al'umma ta daina yi mana wannan tsangwama.
"Me ye laifin hijabi bayan ta suturta mana jiki fiye ma da atamfa?"