Menu

Me ya sa alaƙar Rasha da Kim Jong Un ke neman rikita duniya?

Kim Jon-Un and Vladimir Putin

Wed, 6 Sep 2023 Source: BBC

Ƙasar Amirka da kawayenta sun bayyana rashin jin daɗi game da ziyarar da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ke shirin kai wa Rasha cikin watan nan.

Jami'an Amurka sun bayyana cewar Mista Kim da takwaransa na Rasha za su tattauna yadda Koriya ta Arewa za ta samarwa Moscow makaman da za ta yi amfani da su a yaƙin da take fafatawa da Ukraine.

Moscow na matukar bukatar makamai musamman harsashai da wasu makamai da za ta yi amfani da su a Ukraine.

A nata ɓangaren Koriya ta Arewa wacce take fama da takunkumai tana tsananin bukatar kuɗaɗe da abinci, rufe iyakoki da ƙasar ta yi har tsawon shekaru uku da kuma dakatar da tattaunawar ta da Amurka a shekara ta 2019 sun sa ƙasar ta fuskanci wariya fiye da yadda da fuskanta a baya.

Amurka ta jima ta na tsoratarwa game da kulla yarjejeniyar cinikin makamai tsakanin ƙasashen biyu amma a yanzu sanarwar shirin ganawar Kim Jong Un da Putin ta kara tabatar da haka.

Babban burin Amurka shi ne ɗaukar matakan da za su dakatar da makaman Koriya ta Arewa zuwa fagen yaƙi a Ukraine, yayin da Koriya ta Arewa ta mayar da hankalinta wajen kuɗaɗen da za ta samu bayan sayar da makamai ga Rasha.

Mista Kim zai iya samun riba mai yawa la'akari da yadda Rasha ta ke tsananin bukatar makamai

Masu hasashe na ganin Koriya ta Arewa za ta bukaci taimakon sojoji daga Rasha.

Hukumar Leken Asiri ta Koriya ta Kudu ta bayyana cewar ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya gabatar da bukatar ƙasashen Chaina da Rasha da kuma Korita ta Arewa su gudanar aikin horas da sojojin ruwa na haɗin gwiwa irin wanda Amurka ta yi a Koriya ta Kudu da Japan.

Mista Kim zai iya bukatar makamai daga Rasha a gaba

Babbar bukatar Mista Kim a yanzu ita ce, Mista Putin ya samar masa da fasahar makamai domin taimaka masa wajen samun ci gaba a shirinsa na ƙera makaman nukiliya, musamman tauraron ɗan adam na leken asiri da jirgin ruwa mai ɗauke da makaman nukiliya.

Buƙatar da jami'ai a Seoul suke ganin za ta yi wuyar samuwa saboda kalubalen da za ta iya haifarwa Rasha.

Yang Uk, wani mai nazarin Siyasa a Asiya, ya ce akwai hanyoyin da Rasha za ta taimakawa Koriya ta Arewa ba sai lallai ta cinikin makamai ba,"Idan Rasha ta biya man fetur da abinci, za ta iya farfaɗo da tattalin arzikin Koriya ta Arewa.

Mista Yang wanda masanin tsaro ne ya kara da cewar, "Tsawon shekaru 15 an kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi don dakatar da ita daga ƙerawa da cinikin makaman kare dangi.

To amma yanzu Rasha wacce mamba ce ta din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya za ta iya rusa tsarin gaba-ɗaya.

Yayin da ake ci gaba kakaɓa mata takunkumi, Koriya ta Arewa ta dogara da ƙasar Chaina ne wajen samun abinci da agaji.

A cikin shekarar da ta gabata ne Beijing ta ƙi hukunta Koriya ta Arewa saboda gwajin makaman da ta yi.

Ko ganawar shugabannin biyu za ta yiwu?

Mista Kim ya na ganin yawan tafiye-tafiye a matsayin jefa rayuwa cikin hatsari

Tafiyarsa ta karshe ita ce a watan Fabrairun shekara ta 2019 lokacin da ya ziyarci Hanoi don ganawa da Donald Trump da kuma saduwa da Mista Putin a Vladivostok a cikin watan Afrilu shekarar kuma ya yi amfani da jirgin kasa mai sulke.

Source: BBC