BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Me ya sa kotu ta yi wa 'yar shekara 90 ɗaurin rai-da-rai a Indiya?

Egypt Hanging Hoton alama

Mon, 12 Jun 2023 Source: BBC

A makon jiya ne aka yanke wa wata tsohuwa mai shekara 90 hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda laifin kashe mutum 10 shekara 42 da suka wuce.

'Yan'uwan mamatan sun ce hukuncin ya zo a makare, idan ana batun rage musu raɗaɗi, yayin da su kuma masana shari'a ke kwatanta lamarin da cewa "jinkirin tabbatar da adalci daidai yake da rashin adalci".

Yammacin ranar 30 ga watan Disamban 1981 na ɓata wa dattijan mazauna ƙauyen Sadhupur rai da ke arewacin jihar Utter Pradesh.

"Wani gungun mutane sun shiga gidana misalin ƙarfe 6:30 na yamma kuma suka fara harbe-harbe," a cewar Premvati. Ba ta da tabbas game da shekarunta amma ta ce ta kai kamar 75.

"Ba su tambaye ni komai ba, kawai suka fara sakar mana ruwan harsasai," in ji ta, tana mai cewa lokaci kaɗan, aka kashe 'ya'yanta uku - mai shekara 10 da 8, da kuma mace mai 14.

Premvati ta nuna wa masu ɗaukar hoto da 'yan jarida ƙafar da ta ce an harbe ta bayan lokacin da suka ziyarci ƙauyen bayan kotu ta yi hukuncin. Ciwon ya warke amma har yanzu akwai tabonsa.

'Ya'yanta na cikin 10 mazauna Dalit da aka kashe a yammacin. Premvati na cikin mata biyu da aka raunata a wannan yammaci.

A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu Mai Shari'a Harvir Singh na kotun gundumar Firozabad ya yanke wa mutumin, Ganga Dayal, hukunci wadda ita kaɗai ce ta tsira cikin waɗanda ake zargi, kuma ta fito ne daga ƙabilar Yadav.

An kuma umarci Dayal ya biya tarar rupee 55,000 (dala 668; ko naira 311,288) - idan ya gaza biyan kuɗin, zai ƙara shafe wata 13 a gidan yari.

Alƙalin ya ce tara daga cikin 10 na mutanen da ake zargi sun mutu kafin kammala shari'ar.

Rajeev Upadhyay da ya wakilci gwamnati a shari'ar ya faɗa wa BBC cewa shaidu da yawa ma sun mutu a lokacin.

Premvati da mazauna ƙauyen Dalit sun ce ba sa gaba da kowa. Amma Mista Upadhyay ya ce ana ganin alaƙ ta ɓaci gtsakanin ƙabilun bayan 'yan Dalit sun yi ƙorafi kan wani sahgon sayar da hatsi da ɗan Yadav ya mallaka wanda kuma shi ne ya tayar da rikicin.

Jaridu sun ɗauki labarin sosai a lokacin kuma mazauna ƙauyen sun ce firaministan lokacin, Indira Gandhi da babban ministan yankin Vishwanath Pratap Singh sun ziyarce su, kuma suka yi musu alƙawarin bi musu haƙƙinsu.

Wani jigo a jam'iyyar Bharatiya Janata Party mai adawa, Atal Bihari Vajpayee, ya je ƙuyen don nuna ɓacin ransa game da kisan.

"Ya ce ba zai iya dawo mana da mamatanmu ba, amma ya yi mana alƙawarin bi mana haƙƙinmu," in ji Premvati, kuma ta ƙara da cewa a wurin 'yan jarida mazauna ƙauyen suka ji labarin hukuncin bayan sun je neman martaninsu game da shari'ar.

"Allah kaɗai ya sani ko wannan shi ake kira adalci," kamar yadda ta faɗa musu.

Maharaj Singh, maƙwabcin Premvati wanda shi ma ya rasa 'yan uwa kuma ya taso yana jin labarin "wannan yammacin", ya ce "mun ji daɗi cewa mun samu adalci, amma bai zo a lokacin da ya dace ba".

"An ɗauki shekara 42 kafin ta yi adalci. Da a ce an samu hukuncin a shekara shida ko biyar da magabatanmu sun rasu cikin kwanciyar hankali," in ji shi.

Lauya Upadhyay ya ce an ɗauki lokaci kafin yanke hukuncin saboda ƙauyen da aka aikata kisan yana ƙarƙashin gundumar Mainpuri a lokacin. Amma a 1989, sai aka mayar da shi gundumar Firozabad.

An banzatar da takardun shari'ar a Mainpuri har zuwa 2001 lokacin da aka mayar da su Firozabad bisa umarnin kotun Allahabad.

Har sai a 2021 aka fara sauraron shaidun, in ji Upadhyay, a matsayin wani ɓangare na yunƙurin gwamnati wajen ganin an kammala tsofaffin shari'o'i da gaggawa.

"Gwamnati da sashen shari'a na so su aika saƙon cewa doka za ta yi aiki a kan duk wanda ya aikata laifi," in ji shi.

Sai dai Lauya Akshat Bajpai ya ce dole ne a yi adalci a kan lokaci.

"Tabbas wannan lamari ya yi daidai da jinkirin tabbatar da adalci daidai yake da rashin adalci. Mutane za su iya jure jinkirin shekara biyu ko uku, amma shekara40?"

Mista Bajpai ya ce "gwamnati na da alhakin nema wa mutane adalci a lokacin da ya dace musamman Premvati saboda Dalit ce, ɗaya daga cikin ƙabilun da aka fi zalinta a ƙasar.

Mr Bajpai says "the state has the responsibility to deliver timely justice especially to people like Premvati as they are Dalits who are among the most marginalised people" in the country.

"Gazawa ce ta ɓangaren shari'ar Indiya, inda waɗanda aka zalinta da iyalansu suka zauna jiran shekara 42," a cewarsa.

Ba wannan ce shari'ar da ta ɗauki tsawon lokaci ba kaɗai. Da ma an san tsarin shari'ar Indiya wajen jan-ƙafa kuma 'yan ƙasa da dama na kokawa kan yadda wasu ke shafe shekaru kafin yanke hukunci.

Hakan kan jawo tara dubban shari'o'in da aka kasa ganin bayansu. A watan Fabrairu, gwamnati ta faɗa wa majalisa cewa akwai shari'o'i kusan miliyan 50 da ke gaban kotuna a Indiya.

MA Rashid, wani ƙwararre kan tsarin shari'ar Indiya kuma wanda ya kafa shafin intanet na Live Law, ya ce babban abin da ke jawo tsaiko shi ne ƙarancin alƙalai.

"Ƙiyasin adadin mutanen da suka kamata kowane alƙali ya kula da su a Indiya yana da ƙaranci sosai, kuma adadin da ke kan kowane alƙali a yanzu yana da yawa sosai. Saboda dole shari'a ta ɗauki lokaci."

Mista Rashid ya kuma zargi "tsohon tsari" da ke cin lokaci wajen tantance shaidu - misali, har yanzu alƙalai da hannu suke rubuta shaida duk da cigaban fasaha da aka samu.

Ɗaukaka ƙara, kamar yadda ya ce, a manyan kotuna kan ɗauki aƙalla shekara biyar zuwa 10 kafin a saka su cikin jerin waɗanda za a saurara - sannan su sake ɗaukar kamar haka a Kotun Ƙoli.

"Saboda haka ba sabon abu ba ne a Indiya ku ji an wanke mutum daga zargi a shari'ar da aka ɗauki shekara 20 ko 30 ana yi," kamar yadda ya bayyana.

Source: BBC