Menu

Me 'yan Najeriya ke cewa game da janye haramcin bizar Dubai?

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da Mohammed bin Zayed, Sarkin Imaaraat

Tue, 12 Sep 2023 Source: BBC

Jiragen sama na Kamfanin Emirates Airlines, za su ci gaba da sufuri zuwa Najeriya ba tare da wani ɓata lokaci ba, bayan janye haramta bai wa 'yan Najeriya bizar shiga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin 'yan Najeriya ke ci gaba da bayyana mabambantan ra'ayoyi game da ɗage haramcin.

Labarin dai ga dukkan alamu, ya yi daɗi ga 'yan Najeriya masu kasuwanci da ƙasashen waje da kuma masu zuwa yawon shaƙatawa.

A shekarar da ta gabata ne, hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suka dakatar da bai wa 'yan Najeriya biza bayan kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya dakatar da jigila zuwa ƙasar ta Afirka ta Yamma saboda gazawarsa ta kwashe cinikin da ya yi daga Najeriya.

Daga bisani, shi ma kamfanin Etihad Airlines ya dakatar da zuwa ƙasar.

Najeriya, babbar mai arziƙin man fetur a Afirka, na fuskantar ƙarancin dalar Amurka, abin da ya sa wasu kamfanonin jiragen sama ke shan wahala wajen sayar da tikitinsu a naira, har kuma su iya fitar da dukiyarsu daga ƙasar.

Tinubu ya ɓullo da matakan garambawul da ba a taɓa gani ba cikin gomman shekaru, lamarin da masu zuba jari suka yi maraba da shi.

Shugaban na Najeriya ya janye tallafin man fetur mai cin kuɗi ga gwamnati, sannan ya dunƙule kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

Sai dai a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters har yanzu tsabar kuɗaɗen waje ba su wadata ba a Najeriya. Yayin da farashin dala a kasuwar canji ya zarce abin da ake sayarwa a hannun hukuma.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ɗauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan ranar Litinin a birnin Abu Dhabi.

BBC ta bibiyi mabambantan ra'ayi 'yan Najeriya da suka riƙa bayyana wa a safukan sada zumuntar, ga kuma wasu daga cikinsu:

Bari mu fara da ra'ayin tsohon sanata a jihar Kaduna Shehu Sani, wanda ya ce:

"Ƙoƙarin gwamnati na tattaunawa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa don kawo ƙarshen haramcin biza, abin maraba ne; amma akwai buƙatar jan aiki daga gwamnatin Najeriya wajen bibiyar ayyukan laifi da wasu ke zuwa ƙasar suna tafkawa.

"Sun ɗauki shekaru masu yawa wajen gina ƙasarsu, don haka babu wata ƙasa da ta san abin da take yi, da za ta bari a riƙa tafka laifuka a cikinta.

"Hukumar da ke sanya idanu wajen shige da fice ta Najeriya kamata ya yi ta fitar da jerin sunayen mutanen da ake zargi, ko kuma masu hannu wajen aikata laifukan tarzoma da ta'ammali da ƙwaya ko wata badaƙala domin a dakatar da su tun daga nan.

"Mu ne ya kamata mu fara gyara kanmu".

Sai kuma wani matashi mai suna Prince Adesina, wanda ya yi kira ga 'yan ƙasar su guji cigaba da aikata laifukan da za su iya mayar da hannun agogo baya.

Ya ce "zuwa ga 'yan Najeriya, yayin da kuke fatan zuwa hutu Dubai a watan Disamba, kamata ya yi ku zama masu ɗa'a, don Allah.

"Mutane da dama sun rasa hanyoyin samun kuɗinsu na yau da gobe, saboda dakatar da ba da biza, don Allah mu yi abin da ya dace.

"Allah ya taimaki shugaban ƙasa".

Wasu kuma sun mayar da lamarin na tsokana da barkwanci, inda suke zolayar masu zuwa yawon shaƙatawa Dubai daga Najeriya.

Kamar dai @gimbakakanda

Ya ce "Yayin da aka janye haramcin ba da biza ga 'yan Najeriya, Idan har rabin 'yan ƙasar ba su tafi ba Dubai ba nan da 'yan kwanaki, ba zan ji daɗi ba.

"Yadda wasu ke ta ɓaɓatun a janye haramcin, kai ka ce a can suke samun iskar numfashi. Mu da ba mu da kuɗin zuwa Dubai, muna gefe muna lura da al'amura".

Wata mai amfani da shafin X wanda aka fi sani da Twitter, @hayateey1, ita ma kira ta yi ga 'yan'uwanta 'yan Najeriya cewa su kiyaye da dokokin da aka shimfiɗa.

Ta ce "An janye haramcin biza tsakanin Najeriya da Dubai".

"Don Allah kada a ƙara zuwa a lalata musu ƙasa.

"Kada a ƙara zuwa a haifar musu da matsala, ina roƙon ku.

"Da ku, nake magana".

'An kusa shekara jirgin Dubai bai zo Najeriya ba'

BBC Hausa ta tuntuɓi wani ɗan kasuwa da ke zaune a Dubai kuma jami'i a Ƙungiyar Hausawa mazauna Dubai, Yahaya Ahmed Sira, wanda ya ce ya yi maraba da wannan mataki na janye haramcin.

"Babu wanda ba zai ji daɗin wannan mataki ba, ganin cewa an yi asarar kuɗi masu yawa tsakanin Najeriya da Dubai da kuma tsakanin 'yan kasuwarsu.

"A baya jirgin Dubai na Emirate yakan tashi sau biyar zuwa Abuja da Legas a kowanne mako, amma sanadin wannan haramci, an yi kusan shekara, babu wannan kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

"Asara ce mai matuƙar yawa," in ji Yahaya Sira wanda yake bayani cikin ɓacin rai.

Da yake amsa tambayar, ko waɗanne matakai yake ganin za a ɗauka don ganin ba a sake komawa gidan jiya ba, Yahaya Sira ya ce "Ba aikin kowa ba ne, sai na mahukuntan Dubai.

"Suna da kayan aiki na zamani. Wani lokacin kafin a aikata laifi suke gani su daƙile shi.

Haramcin (a ganina) ya fi ƙarfi a kan tsamin diflomasiyya tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu, maimakon laifukan da 'yan Najeriya ke aikatawa a ƙasar."

Ya kuma ce amma hakan, ba ya nufin ba su da rawar da za su taka domin ƙara taƙaita laifukan da ake zargin 'yan Najeriya suna aikatawa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Samar da babbar ƙungiya ta 'yan Najeriya mazauna Dubai da kuma yin rijista ƙarƙashinta ga duk wanda ke zaune a ƙasar zai taimaka, in ji Sira.

An tambaye shi kan cewa da dama daga cikin 'yan kasuwar da ke zaune a Dubai a baya, sun fara komawa wasu ƙasashe da kasuwanci irin su Turkiyya, shin ko Dubai za ta koma ƙadaminta na baya?

Yahaya Sira ya ce, "Babu shakka Dubai za ta koma kan matsayinta a idon 'yan Najeriya, saboda tsarin da suke da shi na ba da biza, ba iri ɗaya ba ne da sauran ƙasashe.

"Kasashe da yawa na da ƙa'idojin da mai ƙaramin jari kamar miliyan biyar ko bakwai, ba za su iya cikawa ba.

"Amma Dubai babu ruwanta da waɗannan sharuɗan," in ji Yahaya Sira.

Source: BBC