Menu

Me za a yi da gawawwakin mutanen da aka kashe a Khartoum?

Hoton hafsan sojoji a titin Khartoum

Sun, 25 Jun 2023 Source: BBC

Bayan kwashe makwanni bakwai ana gwabza kazamin fada na neman iko da babban birnin kasar Sudan, wasu mazauna birnin Khartoum na kokawa da wata matsala da ba su taba tunanin za su fuskanta ba - me za a yi da gawawwakin da suka taru a kan titunan birnin.

Gargaɗi: Wannan labarin na dauke hotunan da za su iya tayar da hankali.

“Na binne mutane uku a cikin gidajensu, sauran kuma a bakin titin layin da na ke zama,” a cewar Omar, wanda aka sakaya sunansa.

"gewamma hakan da ka bude kofa ka ga kare na na cin bangaren jikin wata gawa"

Babu wanda ya san ainihin adadin mutane da suka mutu a halin yanzu amma ana tunanin sun keta 1000, ciki har da fararen hula da dama da yakin ya ritsa da su.

Inda akwai kungiyoyin soji biyu - rundunan sojojin kasar Sudan da kuma dakarun kungiyar RSF - da ke artabu duk da cewa an yi yarjeniyoyin tsagaita wuta daban-daban, yunkurin zuwa makabarta na tatatere da gagarumin hadari.

Omar ya binne a kalla mutane 20.

"An kashe wani makwabci na a gidansa, babu abin da zan iya yi sai dai na tona kabari a cikin gidan na binne shi," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"An bar gawawwaki na rubewa cikin zafi. Me za iya cewa? wasu ungwanni a Khartoum sun zama tamkar makabarta"

A watan da ya gabata, Omar ya tona kaburbura na mutane hudu a kan titin da ke da kusa da gidansa da ke gundumar al-Imtidad a birnin Khartoum. Ya ce ya san wasu mutanen da suka yi haka a unguwannin da ke kusa.

"Da yawa daga cikin wadanda aka kashe an binne su ne a yankunan da ke kusa da jami'ar Khartoum, kusa da gidan man Seddon, wani sanannen wuri. An binne wasu gawarwakin a unguwannin da ke kusa da titin Mohamed Naguib."

Babu ainhin alkaluman adadin mutanen da aka binne a gidaje ko unguwanni a Sudan, amma Omar ya ce "sun kai gommai".

hamid, shi ma wanda aka sakaya sunansa, ya fuskaci irin wannan lamarin.

Ya shaida wa BBC cewa ya binne sojoji uku a wani yanki na garin Shambat mai tazarar kilomita 12 daga babban birnin kasar, bayan da wani jirgin soji ya yi hatsari.

"Na kasance a yankin kwatsam. Da ni da wasu mutane biyar da mu ka kwashe gawarwakin daga tarkacen, muka binne su a wani wuri da ke kewaye da gidajen mutane."

Hamid, wanda ke sana'ar saida gidaje ya yi shekaru 20 ya na rayuwa a yankin, ya yi imanin cewa wannan "aikin jinkai ne".

"Binne wadanda suka mutu na da muhimmanci" A cewarsa

"Binne su na da muhimmanci. shi ne abin da ya dace a yi. Tafiya zuwa inda makabrata ya ke zai yiya daukan kwanaki kuma maharba sun karade ko ina"

"Mu na kokarin taimakawa al'umma s gujewa barkewan cututtuka". shi ne abin da ya dace a addinance.

'Binne gaskiya'

Shugaban kungiyar likitoci, Dr Atia Abdullah Atia, ya ce duk da kyakkyawar niyyar da mutane ke da shi, wadannan ayyuka na iya lalata bayanan laifukan yaki duk da cewa ba da gangan ba ne.

Ya yi gargadin cewa wadannan hanyoyin binnewa za su iya “binne gaskiya”, ya kara da cewa za a iya lalata alamun yadda mutane suka mutu.

Dr Attia ya ce ya kamata a sami bayanan gawawwaki kafin a binne su a cikin kaburbura a mutunce.

Ya kara da cewa ya kamat mutane su bar harkan binne gawawwaki ga hukumomin lafiya, da kungiyoyin red cress da kuma Red crescent.

''Binne matattu ta wannan hanya bai dace ba. A tsarin binne gawa ya kamata a ce akwai wakilan gwamnati, masu gabatar da kara, kwararrun masu bincike da kuma kungiyar agaji ta Red Cross. Yana da mahimmanci a dauki samfurin kwayoyin halitta, wato DNA."

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yake ganin za a iya bin wadannan tsare-tsaren a kasar da tsarin kiwon lafiya da doka sun durkushe, ya ce ya kamata kasashen waje su taka rawa.

Masu aikin sa kan biyu Omar da Hamid, sun ce su kan dauki hotunan fuskokin gawawwakin da bangarorin jikinsu kafin su binne su, wanda vzai taimaka wuirn tanbtance su nan gaba.

Amma Dr Attia ya yi gargadin cewa rashin ingantacxen binne gawawwaki na iya taimakawa wurin yaduwan cutuka.

“Karnulka na iya hako gawawwakin da aka binna a kaburburan da ba su da zurfi. Ba a amfani da hanyar da ta dace na binne gawa a nan, domin ya kamata sa wani abu mai nauyi ko tubali a kan kabarin don hana hako gawawwakin.” ya shaida wa BBC.

Hamid, ya ce galibin mutanen Sudan sun san hanyar da ta dace na tona kabari inda ake sa gawawwakin "a kalla mita daya a karkashin kasa"

Ana ci gaba da gudanar da wasu shirye-shiryen binne gawarwakin yadda ya kamata.

Wani mutum da mu ke kira Ahmed, mai aikin sa kai da kungiyar Red Cross don kwashe gawawwaki daga tituna.

"Ina daukar hotunan fuska da jiki, ina rubutawa ko sabon gawa ne ko ya dan kwana biyu kuma ina ba shi lamba''.

"I take photos of the face and body, record if it is a new dead body or has decayed [and] give it a number."

Ya ce suna ajiye bayanai kan kowane gawa don tantancewa a nan gaba.

Duk da sukar Dr Atia, mutane na ganin ba su da wani zabi saboda kayayyakin kiwon lafiyar jama'a sun ruguje baki daya.

A ranar 11 ga watan Mayu, wani bidiyo ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda aka binne wasu likitocin Sudan biyu, Magdolin da Magda Youssef Ghali, a lambun gidansu.

Dan uwansu da ba mu bayyana sunansa ba, ya shaida wa BBC a wani sakon bidiyo cewa binne ’yan’uwansa mata biyu a gidan ita ce kawai mafita.

“An bar su kusan kwana 12 ba a binne su ba,” in ji dan’uwan na su, ya na kuka.

"Makwabta sun yi korofi kan wani mummunan wari da ke fitowa daga gidan don haka mutane suka binne su a kabari daya a cikin lambun."

Hukumomin lafiya sun yi aiki tare da kungiyoyin agaji ta Red Cross da Red Crescent ta Sudan don kwashe gawarwakin zuwa makabarta. Sai dai rikicin ya kawo cikas wurin isowar ma su jana'izar.

Yayin da mutane ke kokarin tsira tare da kokarin binne gawawwakin 'yan uwansu cikin mutunci, tunanin wani kotun laifukan yaki ya kasance mai nisa kasancewar halin da ake ciki na tashin hankali da asara.

Labarin ’yan uwan ya nuna irin fargaban da mutane ke fuskanta a kowane rana.

“An binne ’yan uwana mata a rami daya a lambun gidansu, da ban taba tunanin hakan zai zama karshensu ba,” in ji dan uwansu.

Source: BBC