Menu

Mene ne bambancin yin Umrah cikin azumi da sauran lokuta?

Hoton alama

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

Umrah kalma ce ta Larabci wadda ke nufin ziyara, kamar yadda Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu, babban limamin Dutse da ke jihar Jigawa ya bayyana.

Malamin ya ce a shari'ance Umrah na nufin ziyarar ɗakin Allah (Ka'aba) da nufin yin ibada, wadda ta ƙunshi shiga halin Ihrami da Talbiya da Ɗawafi da Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa da kuma aski.

Yin Umrah na ɗaya daga cikin ibadu mafiya tarin lada da al'ummar Musulmai ke yi domin samun gwaggwaɓan ladan da ke tattare da yinsa.

Matsayin Umara a addinin Musulunci

Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu ya ce malaman duniya sun haɗu a kan ra'ayi ɗaya cewa umara abu da da aka shar'anta yinsa.

''Ma'ana abu ne da ya zo a shari'ance ana dalilin a ayi shi''

Sai dai malamin ya ce dangane da matsayinsa a shari'a an samu saɓanin malamai inda wasu ke ganin mustahabbi ne, kamar Imamu Malik da Abu Hanifa.

Sai kuma ra'ayin Imamu Ahmad bin Hambal da Imamu Shafi'i waɗanda suke ganin wajibi ne yin umara amma sau ɗaya a rayuwar mutum, ba kowacce shekara ba.

''Lallai Umrah tana cikin ibadu masu muhimmanci, don haka yana da kyau mutum ya samu ya yi a ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa'' in ji Malamin.

'Umrah a watan azumi na daidai da aikin Hajji'

Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu ya ce akwai hadisai masu tarin yawa da suka nuna falalar yin umrah

''Yin umara a watan ramadan yana daidai da yin aikin hajji'' kamar yadda Manzon Allah ya bayyana a cikin hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito.

Malamin ya ce a wata ruwayar musulim Manzon Allah ya ce ''Yin Umrah a watan azumi daidai yake yin aikin hajji tare da ni (Manzon Allah).

Sai dai malamin ya ce hakan ba yana nufin idan mutum bai je aikin haji ba, idan ya je Umrah da Ramadan to ya sauke farillar aikin Hajji da ke kansa ba.

‘’Duka malamai ba su fahimci haka ba, aikin Hajji yana nan a matsayinsa na wajibi a kan mutum, sannan kuma wannan lada ya same shi a matsayin wanda ya yi aikin Hajji tare da Manzon Allah’’, in ji Dakta Abubakar sani

Abin da ya wajaba kan mai Umara

Dakta Abubakar Sani ya ce babban abin da ya wajaba mai Umrah ya lura da shi, shi ne ya ƙuduri aniya a zuciyarsa cewa ibada zai je, ba ziyarar ganin gari ko haɗuwa da abokai ba.

Don haka ya kamata mutum ya kyautata niyya, tare da tsarkake zuciya.

Malamin ya ƙara da cewa ''ya kamata mutum ya ƙudurce ibada zai je kuma don Allah zai yi’’.

Rukunan Umrah

Malamin ya ce rukunan aikin Umrah guda uku ne, ba kamar aikin Hajji ba wanda ke da rukunai huɗu

Rukunan sun haɗar da ƙulla niyya tare da shiga Iharami ga maza, mata kuma suka sanya tufafin da zai rufe jikinsu, sai fuska da tafin hannu ne kawai za ta bari a waje.

Sai kuma dawafi zagaye bakwai tare da addu’o’i, daga nan sai sa’ay wato ziyara tsakanin duwatsun safa da marwa har sau bakwai.

Malamin ya kuma yi kira ga masu ziyarar umara da su kyautata niyyar tafiyasru, tare da tsarkake zuciya, kada su tafi domin alfahari.

Abinda ke ɓata Umrah

Dakta Abubakar Sani ya ce babban abin da ke ɓata Umrah mutum shi ne saduwa da iyali a lokacin da mutum ya ɗauki niyyar Umrah, sannan yake cikin Ihrami.

Malamin ya gargaɗi masu ziyarar Umrah da su guji saduwa da iyalansu musamman a lokacin da suka ɗauko niyyar Umrahmatuƙar ba su riga sun kammala Umrahr ba.

Sai dai kuma Malamin ya ce akwai wasu abubuwan da ba a so wanda ke cikin Ihrami ya aikata, waɗanda suka haɗar da sanya turare, ko yin aski ko cire wani abu na gashin kai ko ɗaura aure a lokacin da mutum ke cikin Iharami.

Yawan mutane

Adadin masu ziyarar Umrah a lokacin watan Ramadan na ninninkawa fiye da sauran lokuta.

Wannnan kuwa ba ya rasa nasaba da kwaɗayin dacewa da tarin ladan da ke tattare da yin Umrah a cikin watan na azumi, kamar yadda ya zo a cikin hadisai masu yawa.

Wani sako da shafin Facebook na Haramain Sharifain ya wallafa ranar Laraba ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 1.149 ne suka yi Umraha Masallacin Harami da ke Makka.

Haka kuma a ranar Alhamis shafin ya wallafa a Facebook cewa tun farkon watan Ramadan an samu masu ziyara zuwa Masallacin Annabi da ke Madina fiye da miliyan 21.

Tsadar kujera ga masu ziyara daga ƙasashen waje

Wani bambancin da za a iya ambata shi ne na tsadar kuɗin da ake biya domin yin ziyarar Umrah.

Akan samu tashin farashin kujerar Umrah a lokacin watan azumi fiye da sauran lokuta.

Alal misali a Najeriya masu son zuwa Umrah kan biya wajen Naira 750,000 a lokacin da ba azumi ba, amma a lokacin azumin kuɗin kan kai kusan Naira miliyan 1.5.

Masu sharhi dai na ganin hakan ba ya rasa nasaba da yawaitar masu buƙatar yin ziyarar a lokacin watan azumin fiye da sauran watanni

Source: BBC