BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Mene ne hukuncin sahur ga wanda zai yi azumi?

31791492 Hoton alama

Mon, 3 Apr 2023 Source: BBC

Ma’anar sahur ita ce cin abinci a ƙarshen dare ga wanda ya yi niyyar yin azumi, lokacin shi ne gabanin fitowar alfijir.

Sahur abu ne da addinin Musulunci ya bayar da umarnin a yi, sai dai umarnin ba ya nufin wajibci, wanda zai iya samar da hukunci ga wanda bai yi ba.

A a umarnin an yi shi ne ta fuskar ‘mustahabbi’ wato an so duk wanda zai yi azumi ya yi shi, amma barin shi babu laifi ciki.

Mene ne alfanun da ke cikin sahur? Me kuma addini ya ce a kan sahur? Suna daga cikin tambayoyin da muka yi wa Malam Abu Jabir Abdullah Musa (Penabdul).

Malam ya ce a hadisi maganar yin sahur ta tabbata, cikin wani hadisi da Jabir ɗan Abdallah ya ce Annabi ya ce “duk wanda yake so ya yi azumi to ya yi sahur da wani abIn,”.

Wannan na nuni da cewa lokacin sahur ba sai ka cika cikinka da abinci ba, ko ya ya ne kaci kamar yadda aka umarta.

Mutane sun sha ban-ban, wani idan ya yi sahur da abinci cikinsa lalacewa yake irin wannan ai ba za ka matsa masa cewa sai ya yi sahur ya cika cikinsa ba, ko mai ya sa a cikinsa da lokacin sahur, za a kalle shi a matsayin sahur.

Wani kuma idan bai ci ya koshi ba to ji zai yi bai yi sahur ba, ko kuma zai ƙare yinin a galabaice.

Ko a ɓangaren masana lafiya haka lamarin yake wanda sahur ɗin ya fi abun buƙata a wurinsa shi ne wanda ake so dole sai ya yi, wanda ba ya buƙata ko ruwa da tsagen dabino ya ci za a kalle shi a matsayin sahur.

“Ya tabbata a hadisi cewa Annabi ya wuce da azumi bai yi sahur ba, sai dai wasu malaman na kallon haka tamkar wata keɓaɓɓiyar baiwa ce tasa Shi kaɗai, domin idan aka ce kowa ya yi hakan wani ba zai iya azumin ba.

Hadisi ya tabbata cikin Bukhari da Muslim, Annabi Muhammad Ya na cewa “Ku yi sahur saboda a cikin sahur akwai albarka,” in ji Malam Abdullah.

To wannan albarkar ai babu wanda zai so ya yi rashin ta, kuma ya tabbata cewa lokacin sahur lokacin karɓar addu’a ne, mutum yana kammalawa zai iya ɗaga hannunsa ya yi addu’a wadda ake sa ran karɓaɓɓiya ce.

Babu laifi ga wanda ya ci abinci kamar ƙarfe daya ko biyun dare, sai ya ji ba shi da buƙatar abinci a lokacin sahur, babu komi idan ya wuce da azumi.

Shi dabarar da ya sa aka ce mutum ya ci wani abu shi ne, addinin Musulunci na ƙoƙarin kare lafiya da dukiyoyin mutane, babu yadda za a yi ya sanya wa wani mutum abin da zai zamar masa mushaƙƙa, in ji Malam, Wallahu a’alam.

Source: BBC