BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Messi ba zai buga wasan PSG da Benfica a Champions League ba

15876014 Lionel Messi

Tue, 11 Oct 2022 Source: BBC

Lionel Messi ba zai buga wa Paris St Germain wasan Champions League da za ta kara da Benfica ba a Champions League ranar Talata. Kyaftin din Argentina na yin jinya, shi ya sa ba zai yi wasan na babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai ba da kungiyar Faransa ba. Messi shi ne ya ci Benfica a makon jiya a Portugal a karawar cikin rukuni da suka tashi 1-1 daga baya aka canje shi. Mai shekara 35, bai yi wa PSG karawar da ta tashi 0-0 da Reims ba a gasar Ligue 1 ranar Asabar, wasan da PSG ba ta zura kwallo ba a raga a karon farko a kakar nan a lik. PSG ce ta daya a rukuni na takwas da maki bakwai, iri daya da na Benfica ta biyu, sai Juventus ta uku da Maccabi Haifa ta karshe. Sauran 'yan wasan PSG da ke jinya sun hada da Presnel Kimpembe da Nuno Mendes da kuma Renato Sanches.

Source: BBC