Menu

Messi na cikin 'yan wasa 100 mafi tasiri da TIMES ta lissafa

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi yana cikin 'yan wasa 100 mafi tasiri a 2023 a fannin wasanni da TIMES ta lissafa.

Cikin shekarar 2022, dan wasan Paris St German ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya, kuma na uku jimilla da kasar ta dauka.

Daman kofin duniya ne kadai Messi bai dauka ba daga cikin manyan gasar duniya a tarihinsa na taka leda.

Argentina ta dauki kofin a cikin Disamba a Qatar a bugun fenariti da ci 4-2 a kan Faransa mai rike da na 2018, bayan da suka tashi 3-3.

'Yar wasan zamiyar kankara 'yar Amurka, Mikaela Shiffrin tana cikin jerin 'yan wasa 100 a 2023 da suka fi tasiri a fannin wasanni.

A kakar nan Shiffrin ta kafa tarihin lashe gasar zamiyar kankara da duniya da cin wasa 88, ta zarta nasara 86 da Ingemar Stenmark keda shi a tarihin a baya.

Tsohon zakakurin dan wasan kwallon tennis, Roger Federer ya ce Messi dan wasa ne na daban, wanda ke sawa a kalli tamaula ko ba ka sha'awar wasan.

Wasu daga 'yan wasa 100 mafiya tasiri a 2023 da TIMES ta bayyana sun hada da wanda ya dauki kofi biyu a Super Bowl, Patrick Mahomes.

Sauran sun hada da 'yar Amurka mai wasan kwallon kwando, Brittney Griner da dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe da mai rike da Grand Slam uku a tennis Iga Swiatek.

Source: BBC