BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Messi ne gwarzon La Liga na watan Fabrairu

 117520154 Gettyimages 1207990543 Messi ne gwarzon dan kwallon La Liga na watan Fabrairu

Thu, 11 Mar 2021 Source: BBC

Lionel Messi ne gwarzon dan kwallon La Liga na watan Fabrairu, sakamakon rawar da ya taka a gasar ta Spaniya.

Kyaftin din tawagar Argentina, ya ci kwallo bakwai a watan na Fabrairu, kuma shi ne kan gaba a zura kwallaye a La Liga mai 19 a raga a kakar 2020-21.

Kwallayen da Messi ya ci a watan ya taimakawa kungiyar ta koma ta biyu a teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Atletico wadda za ta buga kwantan wasa da Athletic Bilbao ranar Laraba.

Wannan lambar yabo da ya lashe ya kara haskaka bajintar kyaftin din Barcelona a wasannin da yake yi a Spaniya.

Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 463 a karawa 508 a gasar La Liga, ya kuma zura biyu a raga a wasa da Deportivo Alaves da kuma Elche a watan na Fabrairu.

Messi ya yi takara ne da Alexander Isak da Yassine Bounou da Thibaut Courtois da Alex Berenguer da Nabil Fekir da kuma Jose Luis Morales.

Source: BBC