BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Messi zai koma Inter Miami ta Amurka

Lionel Messi

Thu, 8 Jun 2023 Source: BBC

Lionel Messi zai koma taka leda ƙungiyar ƙwallon ƙafar Amurka ta Inter Miami, bayan ya bar Paris St-Germain a kakar nan.

Tsohon ɗan wasan Barcelona na daf da ƙin amincewa da ƙunshin kwantiragin da Al Hilal ta Saudi Arabi ke shirin gabatar masa.

Yarjejeniyar Miami ta ƙunshi cewa ɗan wasan zai yi haɗakar aikin tallace-tallace da Adidas da kuma Apple.

Messi, mai shekara 35, ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon duniya karo bakwai, kuma ana sa ran shi ne zai sake lashewa a bana, bayan da ya ci kofin duniya.

Wannan ne karon farko da kyaftin din Argentina zai taka leda a wajen nahiyar Turai.

Ya so ya ci gaba da wasa a Turai karin kaka daya, sai dai bai samu wani tayi mai tsoka daga wata kungiyar nahiar ba, wanda zabi ya rage masa ko dai ya koma Inter Miami ta Amurka ko kuma Al- Hilal ta Saudi Arabia.

An yi ta alakanta shi da zai koma Saudi Arabia, inda Cristiano Ronaldo ke murza leda, gasar da Karim Benzema zai fara buga wa, bayan barin Real Madrid.

To sai dai Messi ya zabi ya je ya buga gasar kwallon kafa ta Amurka a Inter Miami, sakamakon salon rayuwa da kwantiragin da ta kunshi manyan kamfanoni, bayan kwallon kafa.

Tsohon kyaftin din Argentina yana da gida a Amurka, wanda ya bayar da shi haya.

Messi ya so ya sake koma wa Barcelona, amma dokar kashe kudi daidai samu da ake kira Financial Play ba za ta bari ya koma Sifaniya ba.

Source: BBC