BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Milan da Inter za su buga Champions League ranar Laraba

Olivier Giroud

Wed, 10 May 2023 Source: BBC

AC Milan za ta karbi bakuncin Inter Milan a wasan farko a daf da karshe a Champions League ranar Laraba.

Milan ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyar da maki 10, bayan da Chelsea ce ta daya mai maki 13.

Daga nan Milan ta doke Tottenham 1-0 gida da waje a karawar zagaye na biyu, sannan ta fitar da Napoli da cin 2-1 gida da waje a quarter finals.

Ita kuwa Inter Milan ita ce ta yi ta biyu a rukuni na uku da maki 10, inda Bayern Munich ce ta yi ta daya da maki 18.

Daga nan Inter ta ci FC Porto 1-0 gida da waje a zagaye na biyu, sannan ta yi waje da Benfica 5-2 gida da waje a karawar quarter finals.

Wasannin da suka buga a bana a 2022/2023

Italian Serie A Lahadi 5 ga watan Fabrairun 2023

  • Inter 1 - 0 Milan


  • Italian Super Cup Laraba 18 ga watan Yunin 2023

  • Milan 0 - 3 Inter


  • Italian Serie A Asabar 3 ga watan Satumba 20222

  • Milan 3 - 2 Inter


  • Wannan shine karo na hudu da kungiyoyin Italiyan za su kece raini a Champions League a tarihi.

    Champions League Laraba 6 ga watan Afirilun 2005

  • Milan 2 - 0 Inter


  • Champions League Talata 13 ga watan Mayun 2003

  • Inter 1 - 1 Milan
  • Champions League Laraba 7 ga watan Mayun 2003

  • Milan 0 - 0 Inter


  • AC Milan tana da Champions League bakwai, ita kuwa Inter tana da guda uku jimilla.

    Source: BBC