Sashen Hausa na BBC yana watsa shirye-shirye guda hudu a kowacce rana, na tsawon minti talatin-talatin a harshen Hausa. Akwai shirin Safe, akwai shirin Hantsi, akwai shirin Rana, sannan kuma akwai shirin Dare, dukkaninsu a lokutta kamar haka. A gajeren zango.
Lokutan su ne: 0530,0630,1400,1930 GMT.
Ga masu saurare a jumhuriyar Niger, ana iya kama shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC kai tsaye a gidan radiyon R-et-M, a kan zangon FM 104.5MHz a birnin Niamey.
Sannan akan kama waɗannan shirye-shirye a gidan Radio Anfani a kan zango 100Mhz a Damagaram da Maraɗi.