BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Mota ta markaɗe mutum takwas a Amurka

Accident Scene Dlop4 Hoton alama

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Mutum takwas sun mutu a jihar Texas ta Amurka bayan mota ta kauce hanya tare da afkawa kan dandazon mutane a tashar hawa mota da ke kusa da matsugunan mutane da suka rasa muhallansu da 'yan ci-rani.

Haɗarin ya auku ne a birnin Brownsville da ke kusa da iyaka da ƙasar Mexico da misalin 08:30 agogon ƙasar.

Akwai kuma wasu mutane biyar da suka jikkata, galibinsu na cikin mumunan yanayi.

An cafke direban motar tare da tuhumar sa.

‘Yan sanda a Brownsville sun ce bincikensu har yanzu bai tabbatar ko da gangan direban ya kutsa cikin mutane ba.

Da fari dai rahotannin kafofin yaɗa labarai a Amurka sun rawaito 'yan sanda na cewa kamar da gangan direban ya kai wa mutanen hari.

Darakta a wata cibiyar harkokin addinin Kirista, Victor Maldonado, ya shaida wa BBC cewa hotunan bidiyon da aka naɗa sun nuna yadda direban motar ƙirar SUV ya karya doka ya kutsa cikin mutane da gudu duk da cewa danja ta dakatar da shi.

Mista Maldonado ya ce kasa da rabin sa'a kafin faruwar lamarin, rukunnin mutane kusan 20 da ke zaune a cibiyar sun je tashar domin jiran mota.

Ya fada wa kafar yaɗa labaran Associated Press cewa akasarin mutanen da haɗarin ya rutsa da su maza ne 'yan Venezuela.

Wasu daga cikinsu na kokarin hawa motar bas a wurin ne domin isa wurare daban-daban da suke zama a yankunan Amurka, wanda dama suna da tikiti.

"Dukkanin ma'aikatan da ni kaina, muna kokarin nuna juriya," a cewar Mista Maldonado cikin yanayi na hawaye.

"Galibin mutanen da ke wannan wuri iyaye mata ne da yara, da maza marasa aure. A kan idanunsu, suka shaida wannan mumunan lamari."

Ya kara da cewa shi bai taba fuskantar wani yanayi na musguna wa 'yan ci-rani ba a birnin, amma an ambato yana shaida wa gidan talabijin na KRGV cewa, mutane sun taru a gaban kofa, tun bayan faruwar lamarin kuma ya shaida wa jami'an tsaro cewa hakan ya faru ne saboda su."

Bayan faruwan hadarin, ‘yan sanda sun ce an kai direban asibiti domin kula da lafiyarsa, sannan an yi masa gwajin kwayoyi da giya. An rawaito cewa yana ta ba wa mahukunta wahala saboda ƙin bayar da hadin kai.

A cewar jami'an da ke kula da iyaka ta Amurka, birnin Brownsville na fuskantar ƙaruwar tuɗaɗar baƙin-hauren a 'yan kwanakin nan.

Mr Maldonado ya kuma shaida wa kafofin yada labarai na cikin gida cewa, a cikin watanni biyu da suka gabata cibiyar Ozanam, da ke bai wa mutane 250 mafaka, yanzu akwai mutane sama da 380 da ke rayuwa kullum a ciki.

Jami'ai a Brownsville sun kaddamar da dokar ta-baci a watan da ya gabata, bayan wasu birane irin su Texas sun aiwatar da makamancin haka.

Source: BBC