Roma da Sevilla za su buga wasan karshe a Europa League ranar Laraba a Budapest.
wannan shi ne wasa na biyu da za kara a tsakaninsu, bayan 2-0 da Sevilla ta yi nasara a gasar ranar 6 ga watan Agustan 2020.
Wadanda suka ci wa Sevilla kwallayen sun hada da Sergio Reguilon a minti na 21 da kuma Youssef En-Nesyri a minti na 44.
Kocin Roma, Jose Mourinho bai taba rashin nasara ba a karawa biyar a wasan karshe a Zakarun Turai.
Ita kuwa Sevilla ta lashe kofi shida daga shida da ta kai fafatawar karshe a Europa League, ita ce kan gaba a yawan daukar kofin.
Mourinho, mai shekara 60 yana da kofin zakarun Turai biyar da ya dauka da suka hada da Champions League biyu da Europa League biyu da kuma Europa Conference League da ya lashe a kungiyar ta Italiya.
A karkashin Mourinho, Inter Milan ta lashe Champions League a 2010 kuma na farko a cikin kaka 45.
Kofin zakarun Turai na hudu da Mourinho ya lashe shine Europa League a Manchester United a 2017.
Idan kuma dan kasar Portugal din ya dauki kofin nan zai sha gaban Giovanni Trapattoni, wanda yake da tarihin cin kofi biyar na zakarun Turai.
Roma, wadda ta doke Bayern Leverkusen a karawar daf da karshe tana ta shida a Serie A, gasar da za a kammalata ranar Lahadi.
Idan Roma ta yi nasarar daukar Europa League na bana, zai ba ta damar buga Champions League a badi.