Menu

Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

 118617206 B45b39d1 8524 4bd6 B7b4 B2f5d531fb63 Hoton wani mai tijara da ke kirga naira a Legas

Mon, 24 May 2021 Source: BBC

Abubuwa da dama ne suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi. A wannan makalar, mun duba mafiya muhimmanci daga cikinsu.

Ma'aikata sun saka Kaduna cikin duhu

A ranar Lahadi ne Jihar Kaduna ta afka cikin duhun rashin wutar lantarki tsawon kwana huɗu sakamakon yajin aikin da ma'aikatan jihar suka shiga.

Mahukuntan hukumar samar da hasken wutar lantarki a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bi sahun yajin aikin inda suka nemi gwamnati da ta janye matakin da ta ɗauka na korar sama da ma'aikata 7,000.

Shugaban Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a jihar, Kwamared Ayuba Magaji Sulaiman, ya ce matakin da suka yi niyyar ɗauka shi ne durƙusar da harkoki a jihar daga ranar Lahadi har tsawon kwana biyar.

Gwamnatin Nasir El-Rufa'a ta ce ta ɗauki matakin rage yawan ma'aikatan jihar ne domin yi wa aikin kyautata aikin gwamnati.

Ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yawan kuɗaɗen da take kashewa duk wata wajen biyan albashi.

'Yan ƙwadagon sun janye yajin aikin gargaɗin na kwana biyar a ranar Laraba bayan gwamnatin tarayya ta shiga tsakani.

Nasir El-Rufai zai kori dukkanin ma'aikatan jinya ƙasa da matakin aiki na 14

Gwamnatin Kaduna ta yi barazanar korar dukkanin ma'aikatan jinya da ba su kai matakin aiki na 14 ba.

Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai, ta sanar da matakin korar ma'aikatan ne a ranar Talata duk da boren da ta ke fuskanta na neman dawo da dubban ma'aikatan da aka kora.

Sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar ta zargi ma'aikatan jinyar da katse iskar oxygen daga wani jariri a asibitin koyarwa na Barau Dikko a ranar Litinin da ƙungiyar ƙwadago ta kira yajin aiki.

Sanarwar ta ce "baya ga gabatar da buƙatar neman a hukunta ma'aikatan ga ma'aikatar shari'a, gwamnati za ta kori dukkanin ma'aikatan jinya da ba su kai matakin aiki na 14 ba saboda yajin aikin da suka shiga ba bisa ka'ida ba."

"An ba ma'aikatar lafiya umurnin ta tallata neman aikin sabbin ma'aikatan jinya cikin gaggawa domin maye gurbin waɗanda aka kora sannan albashinsu za a ba ma'aikatan da suka ci gaba da aiki a matsayin kuɗaɗen lada," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a kori duk wani ma'aikacin jami'ar jihar (KASU) da ya ƙaurace wa aiki.

Sannan kuma gwamnatin ta ba dukkanin ma'aikatun jihar umurnin gabatar da rijistar ma'aikatan da ke zuwa aiki ga sakataren gwamnati da kuma kwamishinan ilimi.

An yi jana'izar Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya

An yi jana'izar sojojin Najeriya 11 da hatsarin jirgin sama ya yi ajalinsu a Jihar Kaduna, ciki har da Babban Hafsan Sajan Ƙasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Hatsarin ya faru ne yayin da jirgin da suke ciki ya faɗo a kusa da filin jirgin sama na Kaduna ranar Juma'a.

An gudanar da jana'izar Musulmai guda shida daga cikinsu a Babban Masallacin Abuja, yayin da aka yi Kiristoci tasu a Babbar Coci da ke Abujar.

Wannan ne hatsarin jirgi na sojojin Najeriya na uku a cikin shekarar 2021.

Ƴan bindiga sun kashe sojoji uku a jihar Neja

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe sojoji uku a ƙaramar hukumar Magama ta jihar, kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai Gwamna Abubakar Bello ya ce an kashe wasu daga cikin ƴan bindigar kuma an gano gawarwakin biyu daga cikinsu lokacin da jami'an tsaro suka bi sahun sauran ƴan bindigar.

Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa al'ummomi 25 da ayyukan ƴan bindiga suka raba da muhallansu sun fara komawa gida a ƙauyukansu da ke ƙananan hukumomin Shiroro da Munya da Mariga.

Gwamnan ya ce yana sa ido kan ƴan gudun hijira a jiharsa kuma ya ce komai na tafiya yadda ya dace.

Sai dai gwamnan ya ce har yanzu akwai barazanar tsaro a wasu yankunan jihar amma ya ce jami'an tsaro na aiki ba dare ba rana don shawo kan matsalar.

Tashin farashin kayayyaki ya ragu a Najeriya

Tashin frashin kayayyaki a Najeriya ya ɗan ragu zuwa kashi 18.12 cikin 100 a karon farko cikin kusan shekara biyu, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa.

Hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar da alƙaluman ne ranar Litinin duk da faɗuwar da darajar Najeriya ke yi a 'yan kwanakin nan.

A watan da ya gabata ne tashin farashin ya kai ƙololuwar tashi da kashi 18.17 cikin 100, abin da ya sa masana ke ganin faɗuwar darajar Naira za ta iya ta'azzara lamarin.

Babban Bankin Najeriya (CBN) yana so tashin farashin ya kasance tsakanin kashi 6 zuwa 9.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Najeriya za ta ƙyale darajar naira ta sake karyewa a farashin gwamnati daga ranar Juma'a mai zuwa a wani yunƙuri na CBN da babu mamaki yana son ya daidaita mabambantan farashin canji ne da ake da su.

Buhari ya koma Najeriya daga Paris

A ranar Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan halartar wani taro a kasar Faransa don tattaunawa kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin nahiyar Afirka, bayan galabaitar da ta yi daga annobar kwarona.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ne ya shirya taron, inda wasu shugabanni daga nahiyar Turai da wasu hukumomi da cibiyoyin kudi, irin su Bankin Duniya suka halarta.

Ranar Lahadi, 14 ga Mayu Buhari ya isa birnin Paris domin halartar taron.

Sheikh Dahiru Bauchi ya amince da Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya

Babban malamin ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a matsayin Khalifa.

Shehin malamin ya amince da naɗin Sunusi lokacin da tsohon sarkin na Kano ya gabatar masa da takaddar tabbatar da naɗinsa a hukumance a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya a ziyarar da ya kai jihar Bauchi, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya tabbatar wa BBC.

A makon da ya gabata aka kawo ƙarshen saɓani da ke tattare da naɗin tsohon Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya a hedkwatar ɗarikar ta duniya a Senegal.

Babban jagoran darikar, Mahi Nyass ne ya tabbatar da naɗinsa lokacin da ya karbi bakuncin tsohon sarkin a wata ziyarar watan azumin Ramadan da ya kai ƙasar.

An ambato Sheikh Dahiru Bauchi na cewa naɗin na Sanusi bai rusa jagorancin sauran shugabannin darikar Tijjaniyya ba, musamman waɗanda marigayi Shiekh Ibrahim Nyas ya naɗa.

Najeriya ta dakatar da bayar da sabon fasfo

Najeriya ta dakatar da bayar da sabon fasfo har sai an gama bai wa waɗanda suka nema nan da mako biyu masu zuwa.

Yayin da yake yi wa 'yan jarida jawabi a Abuja ranar Talata, Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Immigration, Mohammed Babandede ya ce za a fara karɓar buƙatar yin sabon fasfon daga ranar 1 ga watan Yuni.

Babandede ya ce sun ɗauki matakin ne biyo bayan umarnin da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bayar.

"An dakatar da ayyukan bayar da sabon fasfo a ƙasa baki ɗaya har zuwa 1 ga watan Yunin 2021, lokacin da za a fara amfani da sabon tsarin fasfo," a cewarsa.

"An yanke shawarar dakatarwar ce saboda a gama bai wa dukkan waɗanda suka nemi a ba su fasfo ɗin tun daga 17 ga watan Mayu."

Ya ce an rufe baki ɗayan hanyoyin biyan kuɗi har zuwa 1 ga Yuni, sannan za a tura tawaga ta musamman domin kammala aikin.

Najeriya ta karɓi fan miliyan 4.2 cikin kuɗin da Ibori ya sata

Antoni-Janar kuma Ministan Shari'a a Najeriya, Abubakar Malami, SAN ya tabbatar da cewa gwamnatin taryya ta amshi Pan 4,214,017.66 na kuɗin da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya sata.

Mai taimaka wa ministan kan yaɗa labarai, Dokta Umar Jibril Gwandu ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A cewar sanarwar, an aika kwatankwacin kuɗin a Naira zuwa asusun gwamnatin tarayya ranar 10 ga watan Mayun 2021.

Dama dai Abubakar Malamin ya sa hannu kan wata yarjejeniyar dawo da kuɗina amadadin gwamnatin Tarayya.

Malami ya ce wannan matakin na nuna cewa Najeriya na da mutunci a idon duniya kan yadda ta ke amfani da kuɗinta da aka sata wanda ake dawo mata da su, wajen samar da abubuwan more rayuwa ga ƴan ƙasarta.

Kamfanin sufurin jirgin sama na Najeriya zai fara aiki a 2022 - Hadi Sirika

Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya, Hadi Sirika, ya ce sabon kamfanin sufurin jirgin sama na ƙasar zai fara aiki nan da farkon shekarar 2022.

Rahotanni sun ambato ministan na bayyana haka ne a yau Laraba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

"A shekarar nan ta 2021, za mu yi ƙoƙarin yin duk abin da ya kamata, muna sa ran mu fara zirga-zirga a cikin wata huɗu na farkon 2022," in ji ministan.

Ya ƙara da cewa annobar korona ce ta jawo jinkiri game da ƙarasa aikin buɗe kamfanin da kuma fara zirga-zirgarsa, yana mai cewa har yanzu gwamnati ta duƙufa wajen yin hakan.

Sirika ya ce ma'aikatarsa za ta miƙa daftari ga masu ruwa da tsaki nan da mako biyu. A wannan shekarar ne aka tsara jirgin zai fara aiki, a cewar Hadi Sirika.

Source: BBC