Kogin Beledweyne da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijirar Shabelle cike yake da tarkacen robobi da ledeji farare da ruwan lemo da shuɗaye iya ganin ido.
Garin - wanda ke da mazauna kusan 43,000 - a yanzu ya zama kufai yayin da iyalai ke amfani da sanduna domin ficewa daga cikinsa yayin da gidajensu suka nutse sakamakon mummunar ambaliyar da ya shafi yankin Beledweyne da ke tsakiyar Somaliya.
Daya daga cikin mazauna wannan wuri shi ne Ahmed Omar mai shekara 25.
"A lokacin da na zo wannan sansani, ban zo da kaya masu yawa ba. Kowa na gudu ne domin tsira da rayuwarsa. Gado ɗay kawai na iya ɗaukowa, da katifa da wasu kayan amfani 'yan ƙalilan," in ji shi.
Omar ba zai iya tuna adadin kwanakin da ya shafe a wanna sansani ba, to sai dai ya damu matuƙa kasancewar shi ya tsira, amma bai sai san halin da mahaifinsa ke ciki ba.
"Mahaifina na zaune a wajen da ambaliyar ta share hanyar garin. Ya maƙale,'' in ji Omar.
Omar na magana cikin tattausar murya, cewa yana jin yunwa, sai dai ya fi damuwa kan abinda matarsa da 'ya'yansa za su ci. A cikin tantinsu, matar tasa na shayar da ɗanta ɗan wata biyar.
Tun cikin watan Oktoba ne, aka fara samun saukar ruwan sama mai ƙarfin gaske a gabashin Afirka, lamarin da matsalar sauyin yanayi ya ƙara munana shi.
Ambaliyar ta janyo mummunar ɓarna ga Somaliya, saboda ya zo ne bayan farin da aka yi fama shi cikin shekara biyar a jere.
Tubban mutane ne ciki har da ƙananan yara suka mutu sakamakon yunwa da ake fama da ita a ƙasar sanadiyyar rashin yin girbi har na tsawon shekara biyar a jere.
Miliyoyin mutane ne suka bar gidajensu domin neman abinci da ruwan sha. A yanzu da ake samun mamakon ruwan sama, mutane na cikin fargaba sakamakon hasashen ƙarin ambaliya da ake yi a ƙasar.
Akwai cibiyar lafiya a kusa da sansanin na Shabelle, ɗaya ne daga cikin manyan asibitocin yankin. Ma'aikatan lafiya a asibitin sun koka kan yawan marasa lafiyar da ke buƙatar kulawaru
Shugaban ma'aikatan jinya na asibitin Eljalle, Abdulkadir Dahir Afrah, ya ce fiye da rabin mutanen da ke zaune a Beledweyne ne ke buƙatar kulawar lafiya a asibitn.
"Tun lokacin da aka fara ambaliyar, adadin ke ci gaba da ƙaruwa a kowace rana. A baya, mukan samu marasa lafiya da ke fama da matsalolin da suka shafi ari, amma a yanzu muna samun ƙaruwar marasa lafiya, musamman ƙananan yara waɗanda ke fama da cutukan da ake ɗauka daga gurɓataccen ruwa,'' in ji shi.
Ma'aikatan lafiya da ke asibitin sun ce suna lura da marasa lafiyar da ke fama da cutukan taifod da kwalara da zazzaɓin denge.
A baya-bayan nen Mariam Musa ta ce sansanin na Shabelle domin neman magani wa 'yarta.
''Tana fama da cutar amai da gudawa,'' in ji ta.
"Likitoci sun ba ni magungunan da zan ba shi. Amma matsalata ba ni da wadataccen abinci a gida da zan ba ta. Na rasa komai nawa sanadiyyar ambaliyar. Dama tana fama matsalar tamowa sakamakon farin da muka daɗe muna fuskanta''.
Masana yanayi da sauyin yanayi sun ce garin Beledweyne na cikin hatsarin ambaliya saboda yana tsakiyar tsaunuka.
Samun ambaliya ruwa a tuddan Habasha mai makwabtaka da ƙasar, ya sa aka samu kwararar ruwan zuwa kogin Shabelle, wanda ya ratsa tsakiyar garin, lamarin da ya sa kogin ya batse.
Garin ya katsance garin harkokin kasuwanci, to amma a yanzu ambaliyar ta shafe kusan duka yankunan garin.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya gano wasu yankunan garin huɗu da kogin ka iya sake batsewa.
Rahoton ya ce gwamnati na buƙatar gina manyan shingaye domin kare sake aukuwar ambaliyar.
Sai dai shugaban masu aikin raba kayan tallafi na da mabanbancin ra'ayi.
Mohammed Maalim, wanda babban mai bayar da shawara ne a hukumar kai ɗauki lokacin da musufi suka auku na ganin cewa dabara ɗaya kawai ita ce a kwashe mutane daga yankin.
Ya ce "Abin da ya fi kawai shi ne a kwashe mazauna garin a sake gina garin. Wannan ce kawai mafita a yanzu domin abin nan yana ta faruwa. Hakan zai yiwu ne kawai idan akwai niyya daga gwamnati."
Wata matsalar ita ce yadda garin yake a tsakankanin tsaunukua, wanda hakan ke nufin hanyoyin da za a iya amfani da su wajen kai ɗauki ga al'umma sun datse, wanda babban ƙalubale ne.
Maalim ya ƙara da cewa "Lamarin ya jefa mu cikin mawuyacin hali. A ɓangare ɗaya kuma mu ne aka sanya wa ido domin mu samar da mafita a matsayin mu na hokumomi. Kuma muna yin iyakar bakin ƙoƙarinmu - Ina ganin kowa na bakin ƙoƙarin sa a ɓangaren gwamnati."
Maalim ya ce ambaliyar bana ta yi kama da wadda ta mamaye birnin Beledweyne a shekarar 1997, inda ta kashe kusan mutum 450 da tarwatsa sama da mutum 150,000.
A yanzu, hukumomi a Somalia na kira ga ƙasashe da hukumomin duniya su kawo ɗauki ga waɗanda lamarin ya shafa.