Menu

Muna da ƴancin karɓar baƙuncin kofin duniya - Saudiyya

36656440 Flag of Saudi Arabia | File photo

Fri, 8 Dec 2023 Source: BBC

Ministan wasannin Saudiyya ya ce zargin cewa, ƙasarsa na son amfani da gasar cin kofin duniya domin gyara sunanta, ba gaskiya ba ne.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙasar daga masu suka a kan damar da Saudiyya ta samu ta karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya.

Lokacin da yake tattaunawa da BBC a birnin Jidda, Yarima Abdulaziz bin Turki Al Faisal ya ce: "Da yawan masu sukar mu ba su taɓa zuwa Saudiyya ba, ko kuma ba sa bibiyar abin da muke yi."

Masu suka na cewa kashe kuɗin da Saudiyya take yi babu iyaka tana yi ne domin habbaka samar da man da masarautar ke yi, da kawar da tunani kan bayanan da ake da su nata game da 'yancin ɗan'adam da kuma tasirinta kan muhalli.

Amma gwamnatin Saudiyya ta dage kan cewa tana zuba kuɗi ne domin habbaka tattalin arziki, domin share hanya ga masu yawon buɗe ido da sauran mutane su rika shiga ƙasar.

A tattaunawarsa ta farko tun lokacin da ƙasar ta nemi ɗaukar nauyin gasar kofin duniya ta maza ta 2034 da ba ta fuskanci hamayya ba, ministan na Saudiyya ya ce:



  • Saudiyya na "nazartar yiwuwar" ɗaukar nauyin gasar lokacin bazara, duk da cewa akan yi matsanancin zafi a ƙasar.
  • Samun goyon bayan Fifa kan shirin Saudiyya na neman karɓar baƙuncin kofin duniya da babu hamayya cikinsa, ya kawar da duk wani shakku.
  • Ya kare yawan kuɗin da aka kashe a gasar Saudi Pro League da ya kai fan miliyan 750 na sayen 'yan kwallo, ya ce babu wanda yake tambaya lokacin da Premier League ke kashe irin nasu. Ya kara da cewa "babu shakka nan gaba abin da za mu kashe zai fi wannan".
  • Da yake mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da aka fuskanta lokacin da Qatar da ke makwabtaka ta karbi baƙuncin gasar a 2022, kan yadda take tafiyar da lamarin 'yan ci-rani sai ya ce "hakan ba zai maimaitu ba."
  • Ya jaddada cewa "ana maraba da kowa" a wannan lokaci, duk da cewa akwai damuwa daga wasu magoya baya kan cewa luwaɗi haramtaccen abu ne a ƙasar haka kuma 'yancin mata a ƙayyade yake.


Source: BBC