Al’ummar Musulmi da gwamnatocin kasashen da Musulmi ke da rinajye, da suka hada da Iran da Iraqi suna nuna bacin ransu kan wulakanta Qur’ani da ake yi a Denmark da Sweden
‘Yan wata kungiya ta masu ikirarin kishin Denmark ne suka kona Littafin mai tsarki na Musulmi a wajen ofishin jakadancin Iraqi a babban birnin Denmark, Copenhagen.
Algeria ta gayyaci manyan jami’an diflomasiyyar kasar ta Denmark da Sweden, a kasarta domin nuna rashin jin dadinta.
A kan hakan ne kuma ranar Litinin aka rika fitar da kayayyakin da ake yi a kasar Sweden daga kasuwa mafi girma a Qatar.
Matakin da ‘yan kungiyar ta masu tsattsauran ra’ayin rikau da ikirarin kishin Denmark suka dauka na bin sahun masu wulakanta Al-Qur’anin mai girma a kofar ofishin jakadancin Iraqi, a babban birnin kasar ta Denmark, inda suka kona Littafin, maimaici ne na abin da suka yi irinsa a ranar Juma’a da ta gabata inda suka yada abin kai tsaye a shafin Facebook.
A lamarin na Litinin wasu mutum biyu ne masu kin jinin Musulunci suka tattaka littafin mai tsarki sanna suka cinna masa wuta a kusa da tutar kasar Iraqi.
Ma’aikatar harkokin wajen Iraqi ta ce yin hakan na haddasa tsana da tsattsauran ra’ayi su haifar da barazanar gaske ga zaman tare na lumana a cikin al’umma.
A hakan ne daruruwan masu zanga-zanga a Baghdad suka yi kokarin kaiwa ga ofishin jakadancin , Denmark din da ke babban birnin na Iraqi domin huce haushinsu.
Kamar yadda a wancan makon jama’a cikin fushi suka cinna wuta a ofishin jakadancin kasar Sweden a birnin bayan kona Al-Qur’anin a Stockholm, babban birnin na Sweden.
Haka kuma lamarin na Denmark da Sweden ya sa dubban jama’a zanga-zanga a babban birnin Yemen Sanaa, inda Musulmi suka nuna bacin ransu kan barin a yi hakan a kasasshen biyu.
Turkiya ta kira lamarin mummunan cin zarafi ga Qur’ani, yayin da ma’aikatar harkokin wajen Algeria ta gayyaci jakadan Denmark da mataimakin jakadan Sweden domin yin Allah-wadarai da kuma sukar abin.
Ita ma Iran a ranar Asabar ta nuna bacin ranta kan wulakanta Qur’anin da aka yi a baya.
Can a kasar Qatar kuwa rahotanni sun bayyana cewa an fitar da kayayyakin da ake yi ne a kasar Sweden daga babbar kasuwa ta kasar, Souq Al Baladi.
Sai dai a wani sakon Tweeter ma’aikatar harkokin wajen Denmark ta ce, kasar ta yi Alla-wadai da kona Qur’anin da ta ce wasu ‘yan tsiraru suka yi.
Ta kara da cewa, matakin na tsokana wanda kuma abin kunya ne, ba manufa da ra’ayin gwamnatin Denmark ba ne.
Gwamnatin ta kuma yi rokon da kada matakin ya tunzura Musulmi su kai ga mayar damartani da tashin hanakali.
A ranar Asabar a Baghdad sai da jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen hana dandazon masu zanga-zanga kaiwa ga ofishin jakadancin Denmark da ke yankin nan mai tsaron gaske inda yawancin ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a babban birnin na Iraqi, wato Green Zone.
Kafin sannan a ranar Juma’a Sweden ta kwashe ma’aikatan ofishin jakadancinta daga Baghdad bayan da masu zanga-zanga suka far ma ofishin.
Kuma gwamnatin Iraqin ta kori jakadan Sweden daga kasar.
Duka wannan ya kasance ne bayan da ‘yan sandan Sweden suka bai wa wani Kirista dan Iraqi dan gudun hijira, damar kona Qur’ani a babban birnin kasar Stockholm a karo na biyu.
Mutumin ya tattaka Littafin amma kuma bai kona shi ba.
An ba shi damar yin hakan ne bayan da kotuna suka soke haramcin da ‘yan sanda suka yi, bisa dalilin abin da kotunan suka kira ‘yancin gangami.
Tun da farko hukumomin Sweden din sun yi suka ga kona Qur’anin da cewa hakan nuna tsana ne ga Musulunci ko Musulmai.