A karshen makon nan hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta bayyana 'yan wasa 11 a Champions League, amma ba N'Golo Kante.
Ranar Asabar Chelsea ta lashe Champions League, bayan da ta doke Manchester city 1-0 a Porto, Portugal.
Kante ya buga wasa 54 a bana tsakanin tawagar kwallon kafar Faransa da kungiyar Chelsea, wanda ya ci kwallo daya, ya karbi katin gargadi 10.
Dan kwallon tawagar Faransa ya buga wa Chelsea karawar Champions League 12 tun daga farko har wasan da Chelsea ta lashe kofin ta kuma zama zakara.
Sai dai N'Golo Kante shi ne ya zama zakakurin dan wasa a karawar da Chelsea ta yi da Real Madrid gida da waje.
Haka kuma shi ne aka bayyana gwarzon dan kwallo a wasan karshe da Chelsea ta doke City ta lashe Champions League na 2020/21.
Sai dai kuma ranar Litinin ta fitar da 'yan wasa 23, ciki har da Kante dan kwallon tawagar Faransa.
Yadda Chelsea ta buga Champions League a bana ta kuma lashe kofin:
Karawar cikin rukuni
20 October 2020 a gida London Chelsea 0-0 Sevilla
28 October 2020 a waje FC Krasnodar 0-4 Chelsea
04 November 2020 a gida Chelsea 3-0 Rennes
24 November 2020 a waje Stade Rennais 1-2 Chelsea
02 December 2020 a waje Sevilla 0-4 Chelsea
08 December 2020 a gida Chelsea 1-1 FC Krasnodar
Wasannin zagaye na biyu
23 February 2021a waje Club Atletico Madrid 0-1 Chelsea
17 March 2021 a gida Chelsea 2-0 Atletico Madrid
Fafatawar Quarter Finals
7 April 2021 a waje Porto FC Porto 0-2 Chelsea
13 April 2021a gida Chelsea 0-1 Porto
Wasan daf da karshe
27 April 2021 a waje Real Madrid 1-1 Chelsea
5 May 2021 a gida Chelsea 2-0 Real Madrid
Gumurzun karshe a Porto, Portugal
Cikin 'yan wasa 11 da Uefa ta bayyana da suka fi kwazo an samu wasu daga Chelsea da suka hada da Edouard Mendy da Azpilicueta da Antonio Rudiger da kuma Jorginho.
Ita kuwa City tana da 'yan wasa da suka hada da Kyle Walker da Ruben Dias da Ilkay Gundogan da kuma Phil Foden.
Fitattun 'Yan wasa 11 a gasar Champions League ta bana:
Mai tsaron raga: