Menu

Na ji raɗaɗin ciwon kafa a wasan Inter - De Bruyne

Kevin De Bruyne 

Mon, 12 Jun 2023 Source: BBC

Kevin De Bruyne ya fada cewar yana ɗauke da rauni a ƙafarsa a wasan Chamions League da Manchester City ta kara da Inter Milan ranar Asabar.

An sauya De Bruyne a wasan da City ta lashe kofin karon farko a tarihi, kuma na uku a bana, bayan Premier League da FA Cup.

An sauya dan kwallon tawagar Belgium a minti na 35 da take wasan, sakamakon raunin da ya ji a wasan da aka buga a Istanbul.

City ta yi nasarar lashe kofin ne da cin 1-0 ta hannun Rodri a minti na 68, daga baya De Bruyne ya shiga fili aka yi murnar daga Champions League da shi.

Wannan shi ne kofin Zakarun Turai na Champions League na uku da Pep Gueardiola ya dauka, bayan wanda ya ci biyu a Barcelona.

Dan ƙasar Sifaniya ya gwada sa'a a Jamus tare da Bayern Munich, amma bai samu nasara ba, daga nan ya koma Ingila da horar da tamaula.

Inter Milan tana da Champions League uku, sai dai rabon ta da shi tun 2010 ƙarƙashin Jose Mourinho.

City ta ɗauki kofi uku a bana wato Premier League da FA Cup da Champions League kamar yadda Sir Alex ya kafa wannan bajintar a Manchester United a 1999.

City ce ta yi ta ɗaya a Premier League, bayan Arsenal ta yi kwana 248 a matakin mai jan ragama, daga baya ƙungiyar Etihad ta lashe shi na uku a jere na biyar a kaka shida.

Haka kuma City ce ta doke Manchester United 2-1 a wasan ƙarshe ta lashe FA Cup na kakar nan.

Source: BBC