BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Na san ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ku - Tinubu

45651741 Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Tue, 13 Jun 2023 Source: BBC

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al'ummar ƙasar su ɗan ƙara sadaukarwa da kansu domin ceto ƙasar daga durƙushewa.

A cikin jawabinsa na tunawa da Ranar Dimokraɗiyya, shugaba Tinubu ya ce ya san cewa shawarar gwamnatin ƙasar ta janye tallafin man fetur, za ta haddasa ƙarin wahala ga talakawa.

Ya ce "ina jin irin raɗaɗin da kuke ji".

Sai dai in ji shi, wannan shawara ce wadda dole ne sai an ɗauka ta domin ceto Najeriya daga durƙushewa da kuma ƙwato dukiyar ƙasar daga hannun wasu tsirarun mutane marasa kishi.

Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa haƙurinsu ba zai tafi a banza, la'akari da yarda da amanar da 'yan ƙasar suka bai wa gwamnatinsa.

Source: BBC