Mason Mount ya ce gamsuwar da ya yi da bayanin kocin Manchester Erik Ten Hag na yadda zai yi amfani da shi ce ta sa ya bar ƙungiyar da ya taso a cikinta.
Ɗan shekara 24 shi ne na farko da Ten Hag ya ɗauka a bana, a cinikin da aka yi na fan miliyan 55, da ƙarin miliyan biyar na wasu tsarabe-tsarabe.
Mount ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar ne da kuma zaɓin ƙara shekara guda idan ta ƙare.
"Bayan haɗuwa da kocin ƙungiyar ya yi min bayanin shirinsa a ƙaina, sai na ji kamar a fara kakar ta bana yanzu," in ji ɗan wasan Ingilan.
"Ko wa zai zama shaida cewa ƙungiyar ta haɓɓaka ƙarƙashin mai horaswa Erik ten Hag.
"Ina da matuƙar buri, Na san daɗin da ake ji idan an lashe manyan kofuna kuma nasan aikin da ake yi ba dare ba rana. Zan yi komai da ƙarfin iyawata a Manchester United."
Sau uku Chelsea na ƙin amincewa da tayin da United ta yi kan Mount kafin daga baya ta amince.
A bara ƙungiyar ta Landan ta kashe fan miliyan 600 wajen sayan 'yan wasa, amma yanzu dole ta sayar da wasu domin samun sauƙi game da dokar taƙaita kashe kuɗi.
Chelsea ba ta so rabuwa da ɗan wasan da ta raina ba tun yana shekara shida, amma ta gaza cimma matsaya wajen sabunta kwantaraginsa da za ta ƙare a baɗi.
"Ba abu ba ne mai sauƙi barin kulob ɗin da ka taso a cikinsa, amma tafiya Manchester zai sake buɗe wani sabon babin ƙalubale a rayuwata," in ji Mount.
"Ganin na buga wasa da su a baya, na san ƙarfin da ƙungiyar take da shi, zan so zama cikin waɗanda za su riƙa cin manyan kofuna ko da yaushe."
Monut wanda ya ci wa Chelsea kwallo 33 cikin wasa 195 da ya buga wa Chelsea tun bayan zamansa babban ɗan kwallo a 2019, bai samu buga wasu wasanni ba a ƙarshen kakar da ta gabata saboda rauni da ya ji, wanda Blue suka ƙare a na 12, rashin ƙoƙari da suka yi kenan na farko cikin shekara 25.
Mount ya lashe Champions a Chelsea ya kuma buga wasan ƙarshe da ƙungiyar ta yi nasara 1-0 da Manchester City. Ya kuma ci kofun zakarun na duniya na Fifa sannan ya lashe Uefa Super Cup.
Ya buga wa Ingila wasa 36, ya ci kwallo biyar, sannan yana cikin tawagar da Gareth Southgate ya je kofin duniya da ita a 2022 a Qatar.