Menu

Nan gaba kaɗan manhajar ƙirƙirarriyar basira ta CHatbots za ta fi mutum kaifin basira

Hoton alama

Thu, 4 May 2023 Source: BBC

Mutumin da ake gani matsayin jagora a fagen manhajar ƙirƙirarriyar basira ta (AI) ya bar aikinsa, inda ya yi gargaɗi game da ƙaruwar illoli game da bunƙasar da fasahar take yi.

Geoffrey Hinton, mai shekara 75, ya sanar da barin aiki ne a kamfanin Google cikin wata sanarwa da ya aika wa jaridar New York Times, inda ya ce a yanzu ya yi nadamar aikin da ya yi.

Ya faɗa wa BBC cewa wasu illoli na fasahar ƙirƙirarriyar basira, mai zuba zance ta (Chatbot) suna da "mugun ban tsoro".

"A iya sanina yanzu, fasahar ba ta fi mu basira ba. Amma ina jin nan gaba kaɗan za ta iya fin mu."

Dr Hinton ya kuma yarda cewa shekarunsa na da alaƙa da shawararsa ta barin katafaren kamfanin fasahar sadarwar, inda ya faɗa wa BBC: "Na kai 75, don haka lokaci ya yi da zan bar aiki."

Binciken farko na Dr Hinton a kan tsarin koya wa kwamfuta sarrafa bayanai tamkar na ƙwaƙwalwa da zuzzurfan koyo sun share hanya ga fasahohin sadarwa na ƙirƙirarriyar basira kamar manhajar zuba zance ta ChatGPT.

A fagen ƙirƙirarriyar basira, tsarin koyar da kwamfuta yadda za ta yi aiki kamar ƙwaƙwalwar ɗan'adam, ta hanyar koyon abubuwa da kuma sarrafa bayanai.

Suna bai wa ƙere-ƙeren ƙirƙirarriyar basira damar koyon al'amura ta hanyar yin gogayyar rayuwa, kamar yadda ɗan'adam zai yi.

Wannan shi ake kira zuzzurfan koyo.

Masanin kimiyyar kwamfyutar, ɗan asalin Burtaniya mazaunin Kanada kuma mai ilmin halayyar ilhama ya faɗa wa BBC cewa fasahar zuba zance ta Chatbot nan ba da daɗewa ba, za ta iya zarce ƙwaƙwalwar ɗan'adam karɓa da sarrafa bayanai masu yawa.

"Yanzu, abin da muke gani shi ne abubuwa kamar fasahar ta GPT-4, ta dusashe ƙwazon mutum ta fuskar sanin ilmin ɗaukacin harkokin rayuwa.

Ingancinsu wajen kimanta al'amuran rayuwa, bai kai ya kawo ba, amma tuni suna iya kimanta sauƙaƙan al'amuran rayuwa," in ji shi.

"Kuma bisa la'akari da ci gaban da aka samu, muna tsammanin abubuwa za su ƙara inganta da sauri.

Don haka akwai buƙatar mu fara nuna damuwa game da haka."

A wani sharihi da ya rubuta a jaridar the New York Times, Dr Geoffrey Hinton ya nunar da cewa wasu "miyagun mutane" za su iya ƙoƙarin amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wajen aikata "miyagun abubuwa".

Da BBC ta tambaye shi ko zai yi ƙarin haske a kan wannan, ya amsa cewa: "Wannan wani lamari ne mafi muni da zai iya faruwa".

"Ku yi tunani mana, idan misali, wasu miyagun mutane kamar [Shugaban Rasha Vladimir] Putin suka yanke shawarar bai wa mutum-mutumi (mai fasahar ƙirƙirarriyar basira) damar iya fito da ƙaramin burinsu."

Masanin kimiyyar ya yi gargaɗin cewa daga bisani suna iya "zuwa da wani buri kamar su ce 'Ina buƙatar na samu ƙarin iko'".

Ya ƙara da cewa: "A ƙarshe na yarda cewa irin abubuwan ƙere-ƙere masu basira da muke ƙagowa sun sha bamban da basirar da muke da ita.

"Mu, halittu ne masu rai, su kuwa ƙere-ƙeren dijital ne. Kuma babban bambanci shi ne abin da aka ƙera na dijital, ana iya yin nau'o'i da yawa kuma cikin siffa ɗaya, iri ɗaya.

"Duk waɗannan nau'o'i kuma suna iya koyon abubuwa a ɗaiɗaikunsu, amma cikin ƙanƙanin lokaci su baza ilmin a tsakaninsu.

To kamar dai a ce kana da mutum 10,000 ne, kuma da zarar ɗaya ya koyi wani abu, to sauran cikin ƙiftawar ido su san shi. T

A haka waɗannan manhajoji na baki-huta (chatbots) za su iya sanin abubuwa masu tarin yawa fiye da duk wani mutum."

Matt Clifford, shugaban Hukumar Ƙirƙira da Zuzzurfan Bincike ta Burtaniya, da yake bayyana ra'ayin ƙashin kansa game da batun, ya faɗa wa BBC cewa sanarwar Dr Geoffrey Hinton tana "jadadda yadda ƙwazon ƙirƙirarriyar basira na koyon abubuwa yake ƙaruwa cikin sauri".

"Akwai gagarumin ci gaba daga wannan fasaha, don haka wajibi ne duniya ta zuba kuɗi maƙudai kuma cikin gaggawa a fannin tabbatar da amincin ƙirƙirarriyar basira, da mallakar ta," ya ce.

Dr Hinton dai ya bi sahun adadin ƙwararrun da ke ƙaruwa wajen bayyana damuwa game da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) - ta fuskar saurin bunƙasar ta, da kuma alƙiblar da ta dosa.

Ya Kamata Mu Koma Baya

A watan Maris, wata buɗaɗɗiyar wasiƙa - wadda haɗakar gomman mutane a fannin ƙirƙirarriyar basira suka sa hannu ciki har da hamshaƙin mai arziƙi a harkar fasahar sadarwa, Elon Musk - sun yi kira a dakatar da dukkan ƙirƙire-ƙirƙiren da suka wuce na ƙirƙirarriyar basirar da ake da ita yanzu wato ChatGPT.

Ta yadda za a samar da ƙwararan matakan tabbatar da aminci wajen amfani da ita, kuma a iya aiwatar da su.

Yoshua Bengio, shi ma wani wanda ake kira jagora a fagen ƙera manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, wanda tare da Dr Geoffrey Hinton da Yann LeCun suka yi nasarar cin lambar karramawa ta Turin a 2018 saboda aikinsu a fagen tsarin koyar da tunani mai zurfi irin na ɗan'adam ga na'ura, shi ma ya sa hannu a kan wasiƙar.

Mista Bengio ya rubuta cewa dalili shi ne saboda "saurin da ba a taɓa tsammani ba" da ƙere-ƙeren ƙiraƙirarriyar basira ke yi "muna buƙatar mu koma baya".

Sai dai, Dr Geoffrey Hinton ya faɗa wa BBC cewa a "ɗan taƙaitaccen zango" yana jin fasahar ƙirƙirarriyar basira za ta kawo ƙarin alfanu maimakon illoli, "don haka ba na tunanin ya dace a dakatar da bunƙasar ƙirƙirar wannan fasaha," ya ƙara da cewa.

Ya kuma ce gasar da ake yi a duniya, za ta sa da wuya a iya dakatawa.

"Idan kowa a Amurka ya dakatar da bunƙasa ta, China za ta iya yin wani gagarumin fintinkau," in ji shi.

Dr Geoffrey Hinton kuma ya ce shi ƙwararre ne a fannin kimiyya amma ba tsara manufofin gwamnati ba, don haka haƙƙin gwamnati ne ta tabbatar cewa an samar da ƙirƙirarriyar basira da ɗumbin tunani, ta yadda za a iya dakatar da ita idan ta zama maras jin magana".

'A tunkari abin da sanin ya kamata'

Dr Geoffrey Hinton ya nanata cewa ba ya son ya soki lamirin Google, kuma katafaren kamfanin fasahar sadarwar ya kasance mai matuƙar "sanin ciwon kai".

"Alal haƙiƙa ma, zan so na faɗi maganganu masu daɗi game da Google. Amma sai sun fi sahihanci idan ba na aiki da Google."

A wata sanarwa, babban jami'in kimiyyar Google Jeff Dean ya ce: "Mun duƙufa wajen tabbatar da ganin mun tunkari fasahar ƙirƙirarriyar basira cikin sanin ya kamata.

Muna ci gaba da koyo don fahimtar illolin da za su ɓullo daga gare ta, yayin da cikin jarumta muke ci gaba da inganta ta.

"Muhimmin abu ne mu tuna cewa ƙirƙirarriyar basirar zuba zance ta (chatbots) ɗaya ce kawai a cikin fannonin ƙirƙirarriyar basira da ake da su, ko da yake su ne suka fi shahara a yanzu.

Jerin tsare-tsaren lissafi na algorizim sun dogara ne a kan ƙirƙirarriyar basirar da ke ba da umarni kan abin da za ku kalla na gaba a shafukan nuna bidiyo ko fina-finai kai tsaye.

Ana iya amfani da ita wajen ɗaukar sabbin ma'aikata wajen tattace takardun neman aiki.

Ga kamfanonin inshora tana iya lissafa kuɗin da mai inshora ya kamata ya riƙa biyan kamfani duk wata.

Tana iya bincika yanayin lafiyar mutum (duk da yake, likitoci 'yan adam ne har yanzu za su yanke shawara ta ƙarshe).

Abin da muke gani yanzu shi ne bunƙasar shigen ɗaukacin ilhamar ɗan'adam a manhajoji ta yadda za su iya ayyuka masu wahala idan an kawo musu wato - artificial general intelligence - inda za a iya horas da fasahohin da aka ƙera, su yi abubuwa iri daban-daban a cikin iyakar aikinsu.

Ga misali, fasahar zuba zance ta ChatGPT tana iya ba da amsa a rubuce ne ga tambayar da aka yi mata, amma abubuwan da za a iya yi da ita kamar yadda muke gani, ba su da iyaka.

Irin saurin ci gaban da ƙirƙirarriyar basira ke samu yana ɗaure kaI hatta ga waɗanda suka ƙirƙiro ta.

An samu gagarumar bunƙasa, tun lokacin da Dr Geoffrey Hinton ya samar da hoton farko na ƙalailaice tsarin koyon abubuwa daga kwamfuta ta hanyar kwaikwayon ƙwaƙwalwar ɗan'adam a 2012.

Hatta shugaban kamfanin Google Sundar Pichai ya faɗa a wata zantawa ta baya-bayan nan cewa shi ma da kansa bai gama fahimtar duk abin da ƙirƙirarriyar basirarsu ta zuba zance (chatbot) mai suna Bard, ke yi ba.

Kada ku ji da wai, muna cikin jirgin ƙasa ne mai zabga uban gudu yanzu, abin damuwar kuma shi ne wata rana zai fara gina wa kansa layukan dogo.

Source: BBC