BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Newcastle ta saye Gordon daga Everton kan fam miliyan 45

Antony Gordon

Sun, 29 Jan 2023 Source: BBC

Newcastle ta kulla ciniki kuma ta biya Everton fam miliyan 45 kan Antony Gordon.

Matashin dan wasan gaban na Ingila ya haska sosai a Goodison Park, wanda hakan ya sa manyan kungiyoyi rububinsa a bana ciki hadda Chelsea.

Kuma ya bar Everton kungiyar da ya fara wasa tun yana dan shekaru 11.

A wata mai kama da haka Leicester City ta sawo Tete daga Shakhtar Donetsk a matsayin aro.

Dama Tete zaman aro ne a Lyon, kuma daga can kungiyar ta King Power da ta lashe kofin Premier League a 2016 ta karbi aronsa zuwa karshen watan Yuni.

Tete ya buga wa Lyon wasanni 30 ya ci kwallaye takwas, ya kuma taimaka aka ci 10.

Leicester na zaune ne na 14 a teburin Firimiya, maki daya ya rage ta fada yan ukun karshe.

Can kuwa a Brighton Moises Caicedo ya sanar da kungiyar cewa yana son raba gari da ita.

Dama kungiyoyin Chelsea da Arsenal na zawarcin dan wasan tsakiyar na Brighton da Ecuador.

Source: BBC