Menu

Neymar na samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwar kafa

84299039 Neymar ya ji rauni a gasar | Hoton alama

Tue, 14 Nov 2023 Source: BBC

Neymar na murmurewa, bayan tiyatar da likitoci suka yi masa a gwiwar kafa, amma ba a fayyace ranar da dan wasan na Al-Hilal zai koma taka leda ba.

Dan kwallon mai shekara 31 ya fama raunin a lokacin da yake buga wa Brazil wasan neman shiga gasar kofin duniya a watan jiya.

Sai dai wasu na cewa irin raunin da Neymar ya ji, idan an yi wa dan kwallon aiki, yakan dauki wata 10 kafin ya koma murza leda.

Likitan tawagar Brazil, Rodrigo Lasmar, ya ce an yi wa Neymar aiki cikin nasara, ana kuma fatan zai mumure cikin sauri.

An dauki Neymar a kan gadon marasa lafiya a wasan da Brazil ta ci Uruguay 2-0, bayan da tsohon dan kwallon na Paris St Germain ya ji rauni a karawar.

Ya koma buga gasar Saudi Arabia a kungiyar Al-Hial kafin fara kakar bana daga PSG kan fam miliyan 77.6.

Source: BBC