BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Orsato ne raflin wasan Chelsea da Real a Champions League

Daniele Orsato

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

An bayyana Daniele Orsato a matakin wanda zai busa wasan Chelsea da Real Madrid a Champions League.

Kungiyar Ingila za ta karbi bakuncin ta Sifaniya a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai zangon quarter finals.

Real Madrid ce ta yi nasara a wasan farko da ci 2-0 a Santiago Bernabeu ranar Laraba 12 ga watan Afirilu.

Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Karim Benzema da kuma Marco Asensio.

Real Madrid ita ce mai rike da kofin bara na 14 jimilla, ita kuwa Chelsea tana da Champions League biyu.

Wannan shine karo na takwas da Orsato dan kasar Italiya, zai busa wasan Real Madrid a Champions League.

Daga ciki ta yi nasara a hudu aka doke ta wasa uku daga bakwai baya da Orsato ya yi wa Real Madrid rafli a Champions League

Wasannin da Orsato ya busa wa Real Madrid a Champions League:

Leipzig 3-2 Real Madrid 2022/23 karawar cikin rukuni

Real Madrid 3-1 Manchester City 2021/22 daf da karshe, wasa na biyu

PSG 1-0 Real Madrid 2021/22 zagayen 'yan 16 wasan farko.

Chelsea 2-0 Real Madrid (2020/21 daf da karshe wasa na biyu

Real Madrid 1-2 Manchester City 2019/20 zagayen 'yan 16 wasan farko

Galatasaray 0-1 Real Madrid 2019/20 karawar cikin rukuni

Real Madrid 8-0 Malmö 2015/16 wasannin cikin rukuni

Source: BBC