Menu

PFA: Dan wasan Man City, Kevin de Bruyne ya lashe kyautar a karo na biyu

 118819620 Kev Getty Kevin De Bruyne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na bana

Mon, 7 Jun 2021 Source: BBC

Dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na bana da kungiyar kwararrun 'yan wasan Ingila ta zaba, kuma karo na biyu a jere.

Shi kuwa Phil Poden shima na City ya lashe kyautar matashin da ba kamarsa a kakar da aka kammala a Ingila.

Dukkansu 'yan wasan Manchester City suna daga cikin wadanda suka taka rawar da kungiyar ta lashe Premier League na bana, kuma na uku cikin kaka hudu.

De Bruyne, mai shekara 29, shi ne na biyu da ya lashe kyautar a jere, bayan Cristiano Ronaldo da ya fara bajintar a lokacin yana Manchester United.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Belgium, ya ci kwallo shida a gasar Premier ya kuma bayar da 12 aka zura a raga a kakar da aka kammala.

Ya taka rawar gani a wasannin Manchester City, wanda ya ji ciwo a karan hanci a wasan karshe a Champions League da Chelsea ta lashe ranar 29 ga watan Mayu a Porto.

Tun daga lokacin likitoci suka yi masa aiki, ana kuma sa ran zai shiga tawagar Belgium ranar Litinin, domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Turai.

Shi kuwa Foden, mai shekara 21, ya yi wa City karawa 50 a dukkan fafatawa a kakar bana, ya kuma ci kwallo 16.

A kuma cikin watan Satumba ya fara buga wa babbar tawagar Ingila wasa, yana kuma cikin 'yan kwallon da Gareath Southgate ya gayyata gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara cikin watan nan.

Source: BBC