BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

PSG na shirin daukar Ziyech kafin rufe kasuwa

Chelsea Forward, Hakim Ziyech Hakim Ziyech of Morocco

Tue, 31 Jan 2023 Source: BBC

PSG na tattaunawa da Chelsea don duba yiwuwar daukar Hakim Ziyech.

Ziyech na daga cikin yan wasan Morocco da suka haska sosai a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar.

To amma wasa hudu kawai ya buga wa Chelsea a gasar Premier League kawo yanzu a bana.

Kazalika PSG na tattaunawa da Inter Milan kan mai tsaron baya Milan Skriniar, wanda kwantiraginsa ke shirin karewa bana.

Ziyech ne Chelsea ta fara saya, tun bayan da aka dage musu takunkumin sayen yan wasa a 2020.

Kuma ta saye shi ne kan fam miliyan 33 daga Ajax a lokacin.

Yanzu haka Chelsea ta sawo yan gaba da suka hada da Mykhailo Mudryk, David Fofana, Noni Madueke, da kuma Joao Felix, bayan Raheem Sterling da Aubameyang.

Sannan har yanzu kungiyar ta Stamford Bridge na kokarin sayen dan wasan tsakiyar Benfica Enzo Fernandez, yayin da ta sayar wa Arsenal da Joginho kan fam miliyan 21.

Za a rufe kasuwar cinikin yan wasan ne yan awanni masu zuwa.

Source: BBC