BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Pele: Shugaba Lula ya isa dandalin jana'iza a Santos

28183481 Shugaba Lula da Silva ya shiga jerin masu makokin mutuwar shahararren dan kwallon duniya Pele

Tue, 3 Jan 2023 Source: BBC

Sabon Shugaban Brazil Lula da Silva, ya shiga jerin masu makokin mutuwar shahararren dan kwallon duniya Pele.

Al'umma daga ko'ina a fadin Brazil da ma baki daga kasashen waje na ci gaba da jerin gwano tun ranar Litinin, don yin tozali da gawar Pele da aka girke a filin wasan Santos.

Lula, wanda ya kama aiki ranar Lahadi, ya tsaya a gaban gawar Pele, inda ya rungume matar mamacin da sauran iyalansa.

Baya ga Shugaba Lula, Shugabanni a duniyar kwallon kafa da suka hada da na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino duka sun hallara a filin don yin ta'aziyya.

A ranar Litinin ne Infantino ya fadi cewa, za su nemi duka kasashen duniya da su saka wa wani filin kwallo a kasarsu sunan Pele, don martaba shi.

Kazalika akwai tsofaffin yan wasa da na yanzu a wurin jana'izar, da suka hada da Ze Roberto, da Neymar, da Vinicius Junior da kuma dan Pele Edinho.

An kuma nuno matasan yan wasan Santos, kungiyar da Pele ya fara wasa a matsayin kwararre, suma suna alhinin mutuwar mutumin da suke so su gada.

Source: BBC