Tsohon golan Manchester United, Peter Schmeichel ya bai wa Andre Onana shawara kan yadda ya kamata ya nuna kansa a Old Trafford.
United ta dauki Onana, golan tawagar Kamaru a bana daga Inter Milan, bayan da ya yi aiki tare da Erik ten Hag a Ajax.
Schmeichel ya koma Old Trafford a 1991 daga Brondby karkashin Sir, Alex Ferguson, wanda shine kyaftin a lokacin da United ta duki kofi a 1999 har da cin Bayern Munich a Champions League.
Mai shekara 59 ya ce ''Manchester United babbar kungiya ce, girmanta ya haura na Inter da Ajax.''
''Duk wani abin da kayi na kwazo ko kuskure nan da nan zai gwauraya duniya. Hakan ba zai yi wu ba a Inter, sai dai wasu wuraren su ji labari.
''Ina jin ya taka rawar gani a Inter a kakar da ta wuce. Ya je Italiya ya karbe gurbin golan Slovenia, Samir Handanovic, ya kuma kai kungiyar wasan karshe a Champions League.
''Saboda haka wasa ne na 'yan kwallo 11 kowa yana bayar da gudunmuwarsa a fili, hakan ne zai kai kungiya ta samu sakamakon da take bukata.''
''Ya kamata ka kwan da sanin dalilin da kungiya ta dauko ka, kuma tana halin da take bukata na komawa kan ganiya - daya daga fitattu a fannin tamaula a duniya.
Ana sa ran Onana zai fara tsare ragar United ranar Litinin a Old Trafford da za ta karbi bakuncin Wolverhampton a wasan farko a Premier League.