BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Pochettino na nuna damuwa kan jinyar Nkunku

75552542 Nkunku

Fri, 12 Jan 2024 Source: BBC

Kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya ce ya damu da koma bayan da jinyar da Christopher Nkunku zai yi fama da ita.

Wasa ɗaya ɗan wasan ya buga a Chelsea a Premeir bana, tun bayan komawa ƙungiyar.

Ciwon gwiwar da ɗan wasan ya ji ya sanya shi jinyar watanni uku, kuma bai bugawa Chelsea wasa biyun da ta yi a baya ba sakamakon raunin da ya ji a kwankwaso.

"Ba dadi abin ya dame mu, muna buƙatarsa a ƙungiyar a yanzu," in ji Pochettino.

"Ana ci gaba da duba lafiyarsa, amma ba musan me yake faruwa ba ya zuwa yanzu.".

Dan wasan Faransan ya ci wa Chelsea kwallo a wasansa na Premier tilo da ya buga, suka yi nasara da ci 2-1 kan Wolves a ranar 24 ga watan Disamba, kuma kwana uku gabanin nan da shi aka fara wasan Crystal Palace.

Amma raunin da ya ji a kwankwasonsa ya sanya Nkunku bai buga wasan FA da muka ci Middlesbrough a ranar Talata.

Source: BBC