Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Chelsea da Leicester kan halin rashin da'a da suka nuna a wasan da suka yi a Premier a bana.
An ci tarar kungiyoyin biyu fam 22,500 kowacce, bayan da suka kasa tsawatarwa 'yan wasansu a karawar da suka yi a Premier League cikin watan nan.
Ranar 18 ga watan Mayu aka tuhumi kungiyoyin biyu, sakamakon yamutsi da suka yi a wasan da Chelsea ta yi nasara a kan Leicester City 2-1 a Stamford Bridge.
Lamarin ya faru ne a daf da za a tashi daga karawar, bayan da mai tsaron bayan Chelsea, Antonio Rudiger ya ture Ricardo Pereira na Leicester City wanda ya yi wa Ben Chilwell.
Chelsea ta kare kakar bana a mataki na hudu a teburin Premier League duk da doke ta da Aston Villa ta yi 2-1 a wasan karshen gasar.
Ita kuwa Leicester City wadda ta lashe FA Cup a bana a karon farko a tarihi, ta kammala Premier ta kakar nan a mataki na biyar, bayan da Tottenham ta doke ta 4-2.
Manchester City ce ta lashe Premier League na bana, Manchester United ta yi ta biyu, sai Liverpool ta uku.