BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Premier League: Konate zai yi jinyar makonni uku

 118666168 Ibrahimakonate Ibrahima Konate

Tue, 31 Jan 2023 Source: BBC

Mai tsaron bayan Liverpool Ibrahima Konate zai shafe sati uku yana jinya, bayan raunin da ya samu a wasansu na kofin kalubale da Brighton.

Ana sa ran ba zai buga wasannin Premier League da kungiyarsa za ta buga ba da Wolves, Everton, da kuma Newcastle.

Kazalila da wahala mai tsaron bayan Faransar ya buga wasan zakarun Turai da Liverpool za ta yi da Real Madrid ranar 21 ga watan Fabrairu.

Yanzu haka Liverpool na wasa ba bu Virgil van Dijk, da Luis Diaz, da Roberto Firmino da kuma Diogo Jota.

Mai tsaron bayan Netherlands Van Dijk wanda yana cikin kashin bayan Liverpool, ya samu rauni ne farkon wannan watan, kuma likitoci sun ce zai shafe sama da wata guda yana jinya.

Lamarin zai iya sa Liverpool ta fasa sayar da Nat Phillips, wanda kungiyar Galatasaray ta Turkiyya ke nema, yayin da tuni aka dawo da mai tsaron baya Rhys, da ke zaman aro a Blackpool a cikin wannan watan.

Source: BBC